Farashin kwallon yazawa ya yi tashin-gwauron zabo
Sakamakon fitar da kwallon yazawa (kashu) zuwa kasashen waje, an samu tashin farashin mudun ’ya’yan yazawan daga Naira 250 zuwa Naira 700 cikin mako daya. Malam Kabiru Katsina wani dillalin kwallon yazawa, ya shaida wa Aminiya cewa, “Farashin ya yi tashin gwauron-zabo ne domin masu sayen suna tarawa su fitar zuwa kasashen waje sun fara […]
Sakamakon fitar da kwallon yazawa (kashu) zuwa kasashen waje, an samu tashin farashin mudun ’ya’yan yazawan daga Naira 250 zuwa Naira 700 cikin mako daya.
Malam Kabiru Katsina wani dillalin kwallon yazawa, ya shaida wa Aminiya cewa, “Farashin ya yi tashin gwauron-zabo ne domin masu sayen suna tarawa su fitar zuwa kasashen waje sun fara yawa. Domin ana fitar da shi kasashen duniya da dama. Bayan a ’yan shekaru da suka wuce ana zubar da kwallon yazawan ne in an shanye shi. Amma yanzu sai gashi reshe ya juye da mujiya, inda farashin kwallon ya fi na tuwon yazawan tsada nesa ba kusa ba.”
Ya kara da cewa dillacin yazawan ya kasu kashi uku, akwai masu yawo suna saye daga masu gonaki, akwai dillalai wadanda ake ba su kudi suna sarowa, sannan akwai wadanda suke da babban dakin adana shi inda suke gyara shi kafin su yi fitar zuwa kasashen ketare.
Ya ce yadda ake tsince mai kyau da mara kyau shi ne, ana zuba kwallon yazawan ne a ruwa, mai kyau yana kwantawa a kasa, sai mara kyau ya taso sama, sai a tsince a zubar.
Malam Kabiru ya ce ya dace a kara wayar da kan jama’a don su kara rungumar harkar noma da kokarin fitar da kayan amfanin gona don samun ci gaban kasa.
Ya ce halin da wadansu suka nuna a bara inda aka ba su kudi don su yi sarin kwallon yazawa, amma suka gudu da kudin, hakan ya sanya a bana aka ki ba da kudin, sai dai mutum ya je ya saro sannan a saya a wurinsa. Ya ce hakan ya sa harkar ta fi tafiya cikin tsabt, domin ba cuta ba cutarwa.