Farashin litar man fetur ya kai N950 a Kano
Galibin gidajen man da ke cikin birnin Kano sun kasance a rufe.
Rahotanni na cewa farashin duk lita daya ta man fetur ya kai naira 950 a Jihar Kano.
Wannan na zuwa ne bayan da masu sayar da man fetur din suka kara farashin duk lita daya daga Naira 900 zuwa 950 a wannan Larabar.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa wannan dalili ya sanya masu sana’ar tuƙa Keke NAPEP a cikin birnin Dabo su ma suka ƙara farashin kuɗinsu na jigilar fasinjoji da kusan kashi 100.
- An gano gawarwakin mutum 2 a cikin tafki a Jigawa
- Ɓata-gari sun sace takardun shari’ar Ganduje a Kano
Lamarin dai na zuwa ne ’yan kwanaki bayan kammala zanga-zangar tsadar rayuwa ta #EndBadGovernanceInNigeria da aka gudanar a tsakanin 1 zuwa 10 ga watan Agusta a faɗin ƙasar.
Bayanai sun ce galibin gidajen man da ke cikin birnin Kano sun kasance a rufe yayin da ’yan tsirarun da ke sayar da man sun cika da dogayen layukan ababen hawa.
Sai dai tun kafin soma zanga-zangar wasu gidajen man suka ƙara farashin litar man fetur din daga Naira 780 zuwa kusan Naira 850.
Kazalika, ’yan bunburutu da ke cin kasuwar bayan fage su ma sun ƙara farashin man fetur a dalilin wahalarsa da ake fama da ita a jihar.
Bincike ya nuna cewa ana sayar da litar man fetur a hannun ‘yan bunburutu a tsakanin Naira 1,100 zuwa 1,200.
Ɓangaren masu ababen hawa da suka zanta da wasu kafofin yaɗa labarai, sun bayyana damuwarsu kan tashin farashin.
Sai dai ƙoƙarin da jaridar ta yi na jin ta bakin Shugaban kungiyar dillalan man fetur ta Nijeriya reshen Jihar Kano, Alhaji Gana Girge ya ci tura har zuwa lokacin hada wannan rahoto.