Farashin mai ya kara tsada a duniya saboda rikicin Rasha da Ukraine

Farashin danyen man samfurin Brent ya haura dala 113 a kowace ganga.

Farashin mai ya kara tsada a duniya saboda rikicin Rasha da Ukraine

Matatar mai ta Fatakwal da ke Jihar Ribas

Farashin danyen mai ya kara tsada a ranar Laraba, yayin da ’yan kasuwa suka rungumi man da ba na Rasha ba, wanda zai haifar da tsadar man a Birtaniya.

Danyen mai samfurin Brent – ma’aunin farashin mai a duniya – ya haura dala 113 a kowace ganga, cirawa mafi girma tun watan Yunin 2014.

’Yan kasuwa na shan wahalar sayar da man Rasha, duk da sun sassauta farashi, saboda wahalar dauko man da kuma biyan kudi sakamakon rikicin Ukraine, wanda kuma ya haddasa ninkuwar farashin Gas a duniya.

Kusan kashi 70 na danyen man Rasha babu wanda zai saya, kamar yadda wani kamfanin makamashi na Energy Aspect na Birtaniya ya bayyana.

BBC ya ruwaito ’yan kasuwa dai na tsoron kada su fuskanci fushin hukumomi sakamakon takunkumin da kasashen yammaci suka kakabawa Rasha.