Farashin mai ya karu zuwa Dala 60 a kasuwar duniya
Farashin danyen mai ya tashi a kasuwar duniya sakamakon zanga-zangar nuna kin jinin gwamnati da ake yi a kasar Iran da kuma rage hako shi da kungiyar kasashen da ke da arzikin mai ta OPEC suka yi da kasar Rasha. Kamfanonin hako mai da ke yammacin Texas na kasar Amurka sun sayar da gangar […]

Farashin danyen mai ya tashi a kasuwar duniya sakamakon zanga-zangar nuna kin jinin gwamnati da ake yi a kasar Iran da kuma rage hako shi da kungiyar kasashen da ke da arzikin mai ta OPEC suka yi da kasar Rasha.
Kamfanonin hako mai da ke yammacin Texas na kasar Amurka sun sayar da gangar danyen man a kan Dala 60 da digo 40 bayan da daga bisani ya karu zuwa Dala 60 da digo 74 wanda hakan shi ne mafi yawa tun watan Yunin shekarar 2015.
Shi kuwa danyen man Brent an sayar da shi a kasuwar duniya Dala 66 da digo 80 a kowace ganga amma daga bisani ya tashi zuwa Dala 67 da digo 29 a kowace ganga.