Farashin man fetur a kasuwar duniya zai iya komawa kamar da kuwa?
Ya zuwa yanzu dai farashin danyen man fetur ya fadi a duniya, inda kuma hakan ya shafi tattalin arzikin Najeriya; wanda kuma haka zai iya haddasa matsaloli masu yawa ga al’umma. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko fetur din zai ci gaba da faduwa ne ko kuwa akwai yiwuwar farashin ya dawo yadda […]
Ya zuwa yanzu dai farashin danyen man fetur ya fadi a duniya, inda kuma hakan ya shafi tattalin arzikin Najeriya; wanda kuma haka zai iya haddasa matsaloli masu yawa ga al’umma. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko fetur din zai ci gaba da faduwa ne ko kuwa akwai yiwuwar farashin ya dawo yadda yake ko ma ya dara na da? Wakilanmu sun tattauna da mutane kuma ga abin da suke cewa:
Farashin man zai sake farfadowa – Lawal Nata’ala Daura
Lawal Nata’ala Daura: “Duk da ana ganin cewa akwai wasu abubuwan da ake gani na ci gaban zamani saboda dama ana ganin kungiyar masu arzikin man fetur na duniya suna yi wa dokar Majalisar dinkin Duniya karen tsaye, wanda shi ya sa aka kirkiro da wasu abubuwa na fasahar zamani, wanda zai sa dole masu tattalin arzikin man fetur din su bi doka. Shi ya sa aka bullo da irin wadannan wayoyi na hannu da katinsu da sauran abubuwa makamantan haka; don ganin an sanya su bin doka da oda na Majalisar dinkin Duniya a kan tattalin arziki. Amma duk da hakan, farashin zai sake farfadowa saboda abin ya shafi har da kasafin kudin shekara ga wasu kasashen ciki har da Najeriya.”