Farashin man fetur a kasuwar duniya zai iya komawa kamar da kuwa? 2
Ya zuwa yanzu dai farashin danyen man fetur ya fadi a duniya, inda kuma hakan ya shafi tattalin arzikin Najeriya; wanda kuma haka zai iya haddasa matsaloli masu yawa ga al’umma. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko fetur din zai ci gaba da faduwa ne ko kuwa akwai yiwuwar farashin ya dawo yadda […]
Ya zuwa yanzu dai farashin danyen man fetur ya fadi a duniya, inda kuma hakan ya shafi tattalin arzikin Najeriya; wanda kuma haka zai iya haddasa matsaloli masu yawa ga al’umma. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko fetur din zai ci gaba da faduwa ne ko kuwa akwai yiwuwar farashin ya dawo yadda yake ko ma ya dara na da? Wakilanmu sun tattauna da mutane kuma ga abin da suke cewa:
Martabar fetur za ta iya dawowa – Muhammad Sani
Malam Muhammad Sani danhaire: “Eh! Zai iya farfadowa har ma martabarsa ta dawo, domin in ka lura ai ba tun yau ba ne farashinsa ya taba faduwa ba kuma ya hau. Idan za ka iya tunawa, shekarun baya ma ai an taba samun faduwar farashinsa, wanda har ma sai da ta kai gwamnati ta rika yin zullumi wajen kasafin kudinta na shekara, haka dai aka yi har farashin nasa ya farfado. Don haka ina da kwarin gwiwa nan ba da jimawa ba ne farashin zai sake farfadowa.