Farashin man fetur a kasuwar duniya zai iya komawa kamar da kuwa? 3

Ya zuwa yanzu dai farashin danyen man fetur ya fadi a duniya, inda kuma hakan ya shafi tattalin arzikin Najeriya; wanda kuma haka zai iya haddasa matsaloli masu yawa ga al’umma. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko fetur din zai ci gaba da faduwa ne ko kuwa akwai yiwuwar farashin ya dawo yadda […]

Farashin man fetur a kasuwar duniya zai iya komawa kamar da kuwa? 3
Farashin man fetur a kasuwar duniya zai iya komawa kamar da kuwa? 3

Ya zuwa yanzu dai farashin danyen man fetur ya fadi a duniya, inda kuma hakan ya shafi tattalin arzikin Najeriya; wanda kuma haka zai iya haddasa matsaloli masu yawa ga al’umma. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko fetur din zai ci gaba da faduwa ne ko kuwa akwai yiwuwar farashin ya dawo yadda yake ko ma ya dara na da? Wakilanmu sun tattauna da mutane kuma ga abin da suke cewa:

Farashin zai dawo – Salisu Ibrahim Jibiya
Salisu Ibrahim Jibiya: “Dukkan abin da aka ce na kasuwa ne, to lallai za a samu lokacin da farashinsa zai tashi ko kuma ya fadi kasa warwas. Kuma ba wannan ne karon farko da farashin man ya fadi ba kuma ya tashi. An taba samun haka kuma ya sake tashi fiye da yadda ake tunani.
Su kansu kasashen masu man ba za su bari ya ci gaba da faduwa ba saboda tattalin arzikin nasu sun aza shi kacokan bisa farashin man. Ke nan ba za su bari abin ya dore ba. Misali, ita kanta Najeriyar. Kuma abin ya zo daidai da karshen shekara. Don haka farashin zai sake farfadowa kila ma har ya wuce yadda ake tunani.”