Farashin man fetur a kasuwar duniya zai iya komawa kamar da kuwa? 4
Ya zuwa yanzu dai farashin danyen man fetur ya fadi a duniya, inda kuma hakan ya shafi tattalin arzikin Najeriya; wanda kuma haka zai iya haddasa matsaloli masu yawa ga al’umma. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko fetur din zai ci gaba da faduwa ne ko kuwa akwai yiwuwar farashin ya dawo yadda […]
Ya zuwa yanzu dai farashin danyen man fetur ya fadi a duniya, inda kuma hakan ya shafi tattalin arzikin Najeriya; wanda kuma haka zai iya haddasa matsaloli masu yawa ga al’umma. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko fetur din zai ci gaba da faduwa ne ko kuwa akwai yiwuwar farashin ya dawo yadda yake ko ma ya dara na da? Wakilanmu sun tattauna da mutane kuma ga abin da suke cewa:
Farashin mai ba zai farfado ba – Ibrahim Wadatau
Ibrahim Wadatau Jamalu Rawayya: “Faduwar farashin man fetur ba daga Najeriya kadai ya fara ba, har ma da sauran kasashen Turai. Farashin man fetur ba zai farfado ba, ya ma dinga sauka kasa ke nan. Da farashin ma talaka na shan bakar wahala ina ga ya fadi? Ai gara ma ya dinga faduwa har ma ya kai kasa warwas. Dalilina, ka ga a kasar nan muna da man fetur amma duk da shi talaka har yanzu ya kasa gani a kasa. Kullum addu’ata ya ci gaba da faduwa, domin talakawa su samu sauki. Ita kanta ma gwamnatin za ta samu saukin wasu abubuwan.”