Farashin man fetur a kasuwar duniya zai iya komawa kamar da kuwa? 5
Ya zuwa yanzu dai farashin danyen man fetur ya fadi a duniya, inda kuma hakan ya shafi tattalin arzikin Najeriya; wanda kuma haka zai iya haddasa matsaloli masu yawa ga al’umma. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko fetur din zai ci gaba da faduwa ne ko kuwa akwai yiwuwar farashin ya dawo yadda […]
Ya zuwa yanzu dai farashin danyen man fetur ya fadi a duniya, inda kuma hakan ya shafi tattalin arzikin Najeriya; wanda kuma haka zai iya haddasa matsaloli masu yawa ga al’umma. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko fetur din zai ci gaba da faduwa ne ko kuwa akwai yiwuwar farashin ya dawo yadda yake ko ma ya dara na da? Wakilanmu sun tattauna da mutane kuma ga abin da suke cewa:
Akwai yiwuwar farashin ya karu – Ubale Mukhtar
Malam Ubale Mukhtar: “A ganina, dangane da wannan faduwar farashin mai a kasuwannin duniya da ya yi, wadda ba tare da la’akarin hakan ba, har Gwamnatin Tarayya ta kasafta kudinta a kan kusan Dala 70 da ’yan doriya bisa ganga daya, ai ba komai ba ne domin kuwa akwai yiwuwar sake farfadowar darajarsa. Dalilina na fadar haka kuwa shi ne, ai a baya babu wanda zai yi zaton farashin man zai fadi; to kuwa akwai kyakkaywan zaton farashin kan iya sake tashi sama wanda zai kai ga gwamnati ta cika burinta kan kasafin kudin da ta yi na shekara mai kamawa ta 2015.