Farashin man fetur a kasuwar duniya zai iya komawa kamar da kuwa? 6
Ya zuwa yanzu dai farashin danyen man fetur ya fadi a duniya, inda kuma hakan ya shafi tattalin arzikin Najeriya; wanda kuma haka zai iya haddasa matsaloli masu yawa ga al’umma. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko fetur din zai ci gaba da faduwa ne ko kuwa akwai yiwuwar farashin ya dawo yadda […]
Ya zuwa yanzu dai farashin danyen man fetur ya fadi a duniya, inda kuma hakan ya shafi tattalin arzikin Najeriya; wanda kuma haka zai iya haddasa matsaloli masu yawa ga al’umma. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko fetur din zai ci gaba da faduwa ne ko kuwa akwai yiwuwar farashin ya dawo yadda yake ko ma ya dara na da? Wakilanmu sun tattauna da mutane kuma ga abin da suke cewa:
Ba lallai ne farashin ya farfado ba – Mustapha Ishaka
Mustapha Ishaka Mai Takalma: “A ganina, dangane da faduwar da farashin man fetur ya yi warwas a kasuwannin duniya, har kuma kasar nan ta kasafta kasafin kudinta kan gangar man fetur a kan Dala sama da 70. Ai kasar nan ta yi ga garaje ga dami, domin kuwa ba lallai ba ne darajar man fetur din ta farfado ba kamar yadda ta yi buri.
“Dalilina na fadar haka kuwa shi ne, in aka dubi dalilan da suka haifar da faduwar man fetur din a kasuwannin duniya, ai dalilan sun kusan samun gindin zama domin kuwa abubuwan da Turawa suka gano da suke son su mayar da su makwafin man don amfani da su na nan daram ba su kau ba.”.