Farashin man fetur ya doshi N1,400

Yayin da rikicin gabas ta tsakiya yake ci gaba da ruruwa, tare da ficewar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE) daga ƙungiyar ƙasashen da ke fitar da man fetur (OPEC) a ranar Talata, farashin fetur ya ci gaba da tashi sama.

Farashin man fetur ya doshi N1,400

Farashin man fetur ya fara kusantar Naira 1,400 kan kowace lita a sassa da dama na ƙasar nan, sakamakon rashin jituwa tsakanin Amurka da Iran kan yarjejeniyar tsagaita buɗe wuta wadda ya kamata ta kai ga sake buɗe mashigar ruwa ta hormuz.

Yayin da rikicin gabas ta tsakiya yake ci gaba da ruruwa, tare da ficewar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE) daga ƙungiyar ƙasashen da ke fitar da man fetur (OPEC) a ranar Talata, farashin fetur ya ci gaba da tashi sama.

daga dalar Amurka  $105 kan kowace ganga a ranar litinin, ɗanyen man fetur na brent ya yi tsallaka zuwa dala $118 a ranar laraba. sakamakon haka, matatar man dangote ta ƙara farashin loda man fetur daga N1,200 zuwa N1,275.

ƙarin bayani kan farashin

Bayanai da aka samo daga Petroleumprice.ng da kuma tabbaci daga wani jami’in matatar man Dangote a ranar Laraba, sun nuna cewa matatar ta ƙara farashin loda fetur zuwa N1,275 kan kowace lita, yayin da farashin samar da shi ta teku ya tashi zuwa N1,215 kan kowace lita.

Wata majiya da ke da masaniya kan lamarin ta bayyana cewa matatar ta dakatar da tsarin bayar da takardar biyan kuɗi (pro forma invoice) tun misalin ƙarfe 4 na Yammacin ranar Talata, lamarin da ya kawo cikas ga tsarin raba mai. Wannan dakatarwa ta haifar da tsayawar sayar da fetur da dizal ga ’yan kasuwa nan take.

Halin da gidajen mai ke ciki

Jaridar The PUNCH ta yi hasashen cewa wannan cigaba na nuni da cewa matatar man Dangote za ta sayi ɗanyen mai a kan farashi mai girma, wanda hakan zai ƙara farashin fetur sama.

An lura cewa gidajen mai ba su ɓata lokaci ba wajen ƙara farashin sayarwa daga matsakaicin farashin N1,250 zuwa sama da N1,300 a ranar Laraba a Legas da sauran jihohin Kudu-maso-Yamma. Binciken jaridar ya nuna cewa gidajen mai a Legas da jihar Ogun sun sayar da fetur a kan farashi tsakanin N1,315 zuwa N1,350 ya zuwa ranar Laraba.