Farashin man fetur ya haura N1,000 a Kaduna
A jihar Kaduna an tilastawa masu ababen hawa sayen man da ya kai Naira 1,100 kan kowacce lita daga hannun ‘yan kasuwa.
Ƙarancin man fetur na ci gaba da tsananta a garin Kaduna inda a wannan Alhamis ɗin masu ababen hawa ke sayen litar man a kan Naira 1,100 a hannun ’yan bumburutu.
Aminiya ta ruwaito cewa, yawancin fasinjojin da za su je aiki da wuraren kasuwancinsu sun maƙale, sakamakon ƙarancin man da ake fama da shi a faɗin jihar sannan gidajen mai ƙalilan ne ke sayar da shi.
- Fursunoni 118 Sun Tsere Daga Gidan Yarin Suleja
- An Gaza Samar Da Motocin Lantarki Bayan Watanni 10 Da Cire Tallafin Man Fetur
Galibin gidajen mai ba sa ba da man, kuma ’yan ƙalilan da ke da shi sun tsawwala farashin yayin da suke sayar da duk lita ɗaya a kan Naira 750 zuwa N810.
Sai dai duk da tsadar da man fetur ɗin ya yi, ababen hawa sun kafa dogayen layuka a gidajen man da ke sayarwa.
Wani mazauni mai suna Mohammed Amin, ya ce ya sayi rabin galan na man, wato lita biyu a kan Naira 2, 200.
Ya ce yana tunanin ajiye motarsa tare da neman hanyar yin wani kasuwanci idan matsalar ta ci gaba.
Aminiya ta kuma tattaro cewa, su ma gidajen man suna ribatar ƙarancin da man da ya yi wajen ƙara farashinsu.
Wata mai suna Amina Isa, ta ce takan biya Naira 100 daga gidan mai na NNPC da ke unguwar Millennium City zuwa shatale-tale inda ta ɗauko wani mai Keke NAPEP zuwa inda za ta.
Ta bayyana cewa, “Bayan na jira awa uku ban sami abin hawa ba, ba ni da zaɓi face na hau keke, na biya Naira 300 zuwa wurin da aka ɗauko ni.”
Wani fasinja mai suna Moses Joseph ya ce ya biya Naira 400 maimakon Naira 200 daga Kakuri zuwa Titin Ahmadu Bello.
Haka kuma, Misis Anna Yohanna da ta hau motar bas daga Gonin Gora zuwa babbar Kasuwar Kaduna, ta ce ta biya Naira 500 maimakon Naira 250.