Farashin man fetur ya koma N138.62 ga dillalai —NNPC

Sabbin farashin man fetur da kananzir da kuma gas da NNPC ta sanya za su fara aiki

Farashin man fetur ya koma N138.62 ga dillalai —NNPC

Kamfanin mai na kasa (NNPC) ya kayyade farashin man fetur a kan Naria 138 da kobo 62.

Bisa umarnin na NNPC, daga yanzu masu manyan rumbunan man fetur za su rika ba wa dillalai masu sari kowace litar mai a kan N138.62.

Dillalan za kuma su rika sayen kananzir a kan Naira 160 kowace lita.

Manajan Kasuwanci a kamfanin sayar da albarkatun mai na NNPC (PPMC), Mohammed Bello a cikin sanarwa ya ce sabon farashin zai fara aiki ne daga ranar Laraba 5 ga watan Agusta 2020.

Danarwar ta kara da cewa za a rika sayar wa su masu manyan rumbunan mai kowace litar man fetur a kan Naira 113 da Kobo 70.

Man gas kuma za a rika ba su kowace lita a kan  N160 a Legas, a Oghara kuma a kan N165.

Sia dai har yanzu hukumar kayyade farashin albarkaun mai (PPPRA) ba ta fitar da mizanin farashin da gidajen za su rika sayarwa ga masu ababen hawa ba.