Farashin man fetur ya yi tsadar da bai taba yi ba cikin shekara 10

Farashin danyen mai ya yi cirawar da bai taba yi ba cikin shekara 10.

Farashin man fetur ya yi tsadar da bai taba yi ba cikin shekara 10

Danyen man fetur

Farashin mai da iskar gas sun ci gaba da tashin gwauron zabi a kasuwar duniya, inda a yanzu farashin ganga daya ta danyan man samfurin Brent ya kai dala 119, cirawa mafi girma cikin shekara 10.

A Turai ma farashin gas na ci gaba da tashi ba kakkautawa, kamar yadda farashin manyan kayayyaki irin su goran-ruwa wato aluminium, da kwal da alkama su ma ke kara tashi.

Duk da cewa Amurka ba ta sanya cinikin mai da gas na Rasha cikin takunkumin da ta jagoranci sanya wa kasar ba a kan mamayar ta a Ukraine, zuwa yanzu ana dari-dari sosai a fannin ciniki da huldar kudade, wajen sayen kayayyakin Rasha.

Karin manyan kamfanonin duniya da kungiyoyi na takaitawa ko ma dakatar da harkokinsu a Rasha.

Kamfanoni na baya-bayan nan su ne IKEA, da Volswagen, da Spotify, da Citigroup, da H&M, da kuma uwa-uba Bankin Duniya.