Farashin masara ya fadi

Sakamakon shigowar kaka da kuma dimbin  noman da jama’ar kasar nan suka yi tare da samun damina mai albarka a bana, yanzu farashin masara wadda ita ce abinci da talakawa suka fi ci da kuma shinkafa da sauran kayayyakin amfanin gona sun fadi kasa sosai  kasuwannin kasar nan. A babbar kasuwar hatsi ta garin Saminaka […]

Farashin masara ya fadi

Sakamakon shigowar kaka da kuma dimbin  noman da jama’ar kasar nan suka yi tare da samun damina mai albarka a bana, yanzu farashin masara wadda ita ce abinci da talakawa suka fi ci da kuma shinkafa da sauran kayayyakin amfanin gona sun fadi kasa sosai  kasuwannin kasar nan.

A babbar kasuwar hatsi ta garin Saminaka da ke Jihar Kaduna, yankin da ke sahun gaba a noman masara a kasar nan, farashin masarar ya fadi da sama da kusan kashi biyu bisa uku idan aka kawatanta da yadda aka rika sayar da ita a lokacin ranin da ya gabata.

Binciken da wakilinmu ya gudanar a kasuwar ya gano cewa a yanzu ana sayar da buhun sabuwar masara da ta bushe, a kan Naira dubu 7, yayin da  ake sayar da buhun tsohuwar masara a kan Naira dubu 8, maimakon Naira dubu 15 da ake sayarwa a kwanakin baya.

Wakilinmu ya kuma gano ana sayar da buhun shinkafa mai bawo kan Naira dubu 8 maimakon Naira dubu 12 da ake sayarwa a kwanakin baya. Kazalika wakilinmu ya gane wa idonsa yadda baki masu sayen kayayyakin amfanin gona daga wurare daban-daban suka cika kasuwa ana ta daukar kayayyakin amfanin gona a motoci. Wadansu masu sayen kayan amfanin gona da wakilinmu ya zanta da su, sun bayyana matukar farin cikinsu kan yadda kayan amfanin gonar ya cika kasuwa kuma a  farashi mai rahusa. 

Sarkin Hatsin Babbar Kasuwar Saminaka, Malam Manu Isah Idris ya shaida wa wakilinmu cewa babu abin da za su ce sai dai su yi wa Allah godiya kan ganin wannan kaka. Ya ce babban dalilin da ya kawo faduwar farashin na masara shi ne shigowar kaka da kuma jita-jitar cewa akwai kamfanonin da suka shigo da masara daga waje.  

Ya yi  kira ga manoman su yi taka-tsantsan wajen kawo kayan amfanin gonarsu kasuwa a yanzu, saboda kusan duk manomin da ya kawo kayan amfanin gonarsa kasuwa yana faduwa ne. 

Har ila yau ya yi kira ga gwamnati ta kara tallafa wa manoma domin hakan zai magance rashin aikin yi a kasar nan. Ya ce yanzu kusan dukan mutanen da suke yankunan karkara sun samu aiki ta hanyar rungumar aikin gona. “Don haka gwamnati ta kare amfanin gonar da manoma suka noma, kuma ta hana shigo da amfanin gona zuwa kasar nan,  yin haka ne zai sanya mutane su kara rungumar aikin noma a kasar  nan,” inji shi.

Daga Jihar Kano waklinmu ya ruwaito cewa an samu rangwamen farshin masara a dukan kasuwannin da ke jihar da sauran wuraren da ake sayar da kayan abinci inda ake sayar da kwano guda na sabuwar jar masara a kan Naira 180, maimakon Naira 450, kuma ake sayar da buhunta a kan  Naira 7200. Ya ce ana sayar da kwanon farar masara kan Naira 170 yayin da ake sayar da buhu kan Naira dubu 6800. Sai dai akwai bambancin farashi a tsakanin sabuwar masara da tsohuwar inda ake sayar da kwanon tsohuwar masara Naira 260, yayin da ake sayar da buhu A kan Naira dubu 10 da 400.

Mafiya yawan masu harkar sayar da masara da wakilinmu ya tuntuba sun bayyana wa cewa ana kyautata zaton idan aka kara ci gaba da aikin girbe masarar a sauran wurare za ta kara karyewa musamman ganin yadda damina ta yi kyau a ko’ina a kasar nan.

Wakilinmu ya ce fataken kayan amfanin gona suna kara himma wajen nemo masarar daga sassan kasar nan zuwa kasuwannin da suke sassan Jihar Kano inda suke sayar da itaa farashi mai sauki.