Farashin Rago ya fara haura dubu 200
A yayin da musulmi ke shirin bikin sallar Edil-Kabir a ranar Talata mai zuwa, farashin raguna ya haura a garurruwa daban-daban na kasar nan, sai dai kuma a wadansu wuraren a dan samu rangwame. A Kaduna ragon da ya fi tsada shi ne na naira dubu dari biyu a kasuwar Zango da ke Tudun Wada, Kaduna. […]

A yayin da musulmi ke shirin bikin sallar Edil-Kabir a ranar Talata mai zuwa, farashin raguna ya haura a garurruwa daban-daban na kasar nan, sai dai kuma a wadansu wuraren a dan samu rangwame.
A Kaduna ragon da ya fi tsada shi ne na naira dubu dari biyu a kasuwar Zango da ke Tudun Wada, Kaduna. A cewar mai ragon Malam Yunusa Umar,” An taya ragon naira dubu dari da hamsin amma na hana saboda a wajena yana a kan naira dubu dari biyu ne. Kuma a gaskiya ba na tsammanin akwai wani rago a kasuwar nan ta Zango da ya yi girmansa ko kudinsa. Na kawo wannan ragon ne daga Maiduguri. A bara na sayar da irinsa naira dubu dari biyu da hamsin amma sai ga shi mun sauko kasa saboda yadda kasuwar take, gashi kuma babu kudi a hannun mutane,” inji shi.
Alhaji Saleh Sule shi ne garkuwan Kasuwar Zango a Tudun Wada kuma shi ne shugaban kungiyar Masu sayar da dabbobi a kasuwar, ya ce, “ Gaskiya kasuwar dabbobi ba ta ci kamar yadda ya dace saboda ma’aikata ba a biya su albashi ba. Wannan ya sa dole ne mu yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jaha da su daure su yi wa ma’aikata albashi tun kafin lokaci ya kure,” inji shi.
Daga Legas kuma wakilinmu ya ce, masu sayar da raguna da ke Kudancin Najeriya sun ce tashin farashin da aka samu a wannan shekara ya samo asali ne daga matsalar rashin tsaro da yankin Arewa maso gabashin kasar ke fuskanta.
Shugaban masu sayar da raguna a kasuwar kasa da kasa ta Alaba da ke Legas, Alhaji Umaru Na Gwaggo ya gaya wa manema labarai cewa rikicin ya takaita safarar raguna zuwa Legas, wanda hakan ya sa wadanda aka kawo suka yi tsada.
“A ‘yan shekarun baya ana sauke raguna na doguwar mota kusan dubu biyu, wato idan ana daf da sallah ke nan, amma yanzu haka dogayen motoci 30 ne kawai suka sauke raguna a farkon makon nan da muke ciki.”
A cewar Na Gwaggo hakan ya sa ragunan suka yi tsada inda ragon da za ka saye shi a shekarun baya akan farashin 15,000 yanzu sai ka kashe 25,000 ko ma 30,000.
Har ila yau shugaban ya ce safarar raguna daga kasashen irinsu Sudan da Libiya da kuma Chadi ya shafi kasuwa matuka saboda rikice-rikice da wadannan kasashe ke fuskanta a yanzu.
A Gombe kuma wakilinmu ya ruwaito cewa, wani mai sana’ar kiwo da safarar dabbobi a garin Gombe Usman Mai Gemu, ya danganta hauhawar farashin dabbobi a bana da shigowar baki daga kudancin kasar nan irin jihar Legas. Ya ce akwai dabbobi da yawa bana a kasa amma sai dai babu kudi a hannun jama’a, duk da haka kuma ba sa sauki saboda dabbobin suna da kyau. “A farashin bana wanda muke sayarwa Naira dubu 100, a bara Naira dubu 80 ake sayar da shi wanda kuma ake sayarwa Naira dubu 90 a bana, a bara Naira dubu 65 ne.’’
“Abun da ya kawo tsadarsu a bana shi ne, da sai mun shiga Maiduguri mu wuce mu shiga kasar Nijar ko Chadi mu sayo dabbobin, amma saboda rikici na rashin tsaro a Maiduguri ya sa ba ma iya zuwa wadannan kasashe mu sayo, muke amfani da wadanda muke da su a cikin gida.’’
A Kano kuma Aminiya ta gano cewa farashin dabbobin layya a kasuwannni yana haurewa.
Binciken da Aminiya ta gudanar a kasuwannin dabbobi na ‘Yan awaki da kuma Hauren makaranta da ta Gidan Zoo ya nuna cewa farashin dabbobi ya haura sama idan aka kwatanta da farashin da aka sayar da dabbobin a bara; ragon da aka samu a bara a kan Naira 17,000, a yanzu haka ana samunsa a kan kudi Naira 20,000. Haka kuma san da ake samunsa a kan kudi Naira dubu 80 a bara, a bana ya haura har zuwa Naira dubu 100.
Masu sayar da dabbobin sun alakanta tsadar a kan rashin isassun dabbobi a kasuwanni da kuma karin kudin da ‘yan ka-yi-na-yi ke yi a kan dabbobin.
Sai dai kuma Alhaji Mansur Ashura wanda yake sayar da dabbobi a wannan kasuwa ya bayyana wa Aminiya cewa, “A gaskiya rashin kudi a hannun mutane ya jawo dabbobin sun yi sauki a kasuwanni. A yanzu haka dabbobi ma sun yi kadan a kasuwanni, kasancewar rashin tsaro da ake fama da shi a garin Maiduguri ya hana mutane zuwa dauko dabbobin a Kamaru da Chadi.” Inji shi.
Alhaji Isa wani mai sayar da dabbobi ne a kasuwar Zoo road ya bayyana cewa a kasuwarsu suna da dabbobi iri biyu; akwai wadanda su suka kiwata su da kuma wadanda ake kawowa daga kasashen da ke makwabtaka da kasar nan wanda kuma hakan ya jawo bambancin farashin a tsakanin dabbobin”Dabbobin da muka kiwata sun fi tsada kasancewar mun tsaya mun kula das u da magunguna da abinci da sauran abubuwa na kiwo, akwai kuma wadanda ake kawo mana daga kasashen su Kamaru da Chadi. Za ka ga dabbobi masu girma daya amma sai a samu bambanci a farashin. Naman dabbibin da muka kiwata ya fi lafiya ya fi kuma dadi. Sai dai mutane kadan ne ke gane hakan, domin an fi sayen masu saukin kudi.” Inji shi.
Daga Ibadan kuma Wakilinmu da ya ziyarci babbar kasuwar dabbobi ta Akinyele, dake kusa da birnin Ibadan, ya gane wa idanunsa irin yadda raguna manya da kanana suka cika kasuwar. A daidai wannan lokaci kuma ana ci gaba da sauke ragunan da aka sayo daga Arewacin kasa.
A binciken da wakilinmu ya gudanar ya gano cewa, akwai alamomi da suke nuna cewa farashin raguna za suyi sauki a bana idan aka kwatanta su da bara. Matsalar rashin kudi a hannun jama’a ita ce babbar alama a bayyane da take nuna cewa farashin ragon layya zai yi kasa kasa a bana. Tun kafin zuwan wannan rana mutane da yawa da suka saba sayen raguna 2 zuwa 3 domin yin layya a kowace shekara suke nuna tababar yin haka a bana a dalilin karancin kudi a hannunsu.
Farashin manyan raguna a kasuwar ta Akinyele ya fara ne daga naira dubu 40 zuwa 60, a yayin da ake sayar da kananan raguna a kan naira dubu 20 zuwa 30. Har zuwa ranar laraba ba a iya samun ragon da farashinsa ya kai naira dubu 70 k0 80 a cikin wannan kasuwar Akinyele ta Ibadan ba.
A Bauchi kuma wakilinmu ya ce farashin raguna a bana ya tsawwala, duk da cewa akwai su da yawa a kasuwanni.
A kasuwar dabbobi ta kofar Ran, Malam Halilu Musa Firo, ya bayyana cewa, akwai dabbobi a kasuwar amma babu masu saye, dole sai zuwa karshen mako za a iya fahimtar yadda kasuwar za ta kasance, musamman ganin yadda dabbobi suka yi tsada fiye da bara, lamarin da yake gani ba zai rasa nasaba da rufe kan iyakokin Nijeriya ta gabas ba, day a sanya ba a shigo da su daga kasashen Kamaru da Chadi da kuma yankin kasar Maiduguri kamar yadda aka saba.