Farashin raguna ya tashi a Jos

A ci gaba da shirye-shiryen bikin Sallar Layya, wadda  za a gudanar a ranar Litinin mai zuwa, farashin  raguna ya yi sama a garin Jos babban birnin Jihar Filato, idan aka kwatanta da Babbar Sallar bara.Binciken da wakilinmu ya gudanar a babbar kasuwar dabbobi ta Nasarawa da ke garin Jos, ya gano cewa farashin ragunan […]

Farashin raguna ya tashi a Jos
Farashin raguna ya tashi a Jos

A ci gaba da shirye-shiryen bikin Sallar Layya, wadda  za a gudanar a ranar Litinin mai zuwa, farashin  raguna ya yi sama a garin Jos babban birnin Jihar Filato, idan aka kwatanta da Babbar Sallar bara.
Binciken da wakilinmu ya gudanar a babbar kasuwar dabbobi ta Nasarawa da ke garin Jos, ya gano cewa farashin ragunan sun yi sama. Kodayake, ya fahimci cewa a bana babu ciniki.
A bana farashin ragunan ya kama daga Naira dubu 100 zuwa dubu 50, har ma da na Naira dubu 10. Irin wadannan raguna  a bara  kudinsu ba su kai haka ba.
Da yake zantawa da wakilinmu shugaban kasuwar dabbobi ta Nasarawa da ke  Jos, Alhaji Kawu Muhammad ya bayyana cewa yanayin kasuwar raguna a bana, sai dai su yi wa Allah godiya, domin kowa yana kukan halin rayuwar da ake ciki a kasar nan.
Ya ce  farashin raguna a bana, ya tashi saboda dawainiyar  kudin mota da kudin haraji da ake karba  daga wajen masu sayar da dabbobi. A bara babbar Sallah ta zo ne  bayan an gama aikin gona, amma  bana ba a gama aikin gona ba tukuna, wadansu kuma  sun sayar da dabbobinsu sun sayi abinci.
Ya ce amma “Maganar ciniki a bana babu, saboda halin matsin da ake ciki a kasar nan.”