Farashin ridi ya yi tashin gwauron zabo a Jihar Sakkwato

Ridi na daya daga cikin tsirrai da ake samar da man girki a cikinsa kuma duk kakarsa ta kankama sai dai ana karancinsa a Jihar Sakkwato abin da ya haifar da tashin farashinsa. “Daga yanzu har zuwa tsakiyar shekara za a ci gaba da samun karancin ridi,” inji Shugaban Kungiyar Manoman Ridi na Jihar Sakkwato, […]

Farashin ridi ya yi tashin gwauron zabo a Jihar Sakkwato

Ridi na daya daga cikin tsirrai da ake samar da man girki a cikinsa kuma duk kakarsa ta kankama sai dai ana karancinsa a Jihar Sakkwato abin da ya haifar da tashin farashinsa.

“Daga yanzu har zuwa tsakiyar shekara za a ci gaba da samun karancin ridi,” inji Shugaban Kungiyar Manoman Ridi na Jihar Sakkwato, Alhaji Umaru Falke Tambuwal.

Ya ce, ana noma ridi sau uku a shekara daga watan Yuli zuwa Satumba da Oktuba zuwa Nuwamba da Janairu zuwa Maris, kuma  a wannan lokaci ne ake samun karancinsa a jihohi musamman ga masu fita da shi don sayar wa masana’antu.

“Muna da manoman ridi sama da 4000 a kananan hukumomin da aka fi noma shi a Sakkwato su ne, Sabon Birni da Isa da Wurno da Dange-Shuni da Tureta da Goronyo da Tambuwal, duk da haka mutanenmu  na bukatarsa domin bukatu daban-daban mun kasa wadatar da su a Sakkwato,” inji shi.

Ya ce, ba ka gane irin ridi yana da daraja sai ka shiga kasuwa nemansa, buhu daya ana samunsa kan Naira dubu 25 zuwa dubu 30 in aka noma kuwa zai tashi daga dubu 40 zuwa dubu 50, tashinsa ya danganta da yawan nemansa inji ’yan kasuwa.

Alhaji Falke ya koka kan rashin kananan masana’antu na gida da za su rika karbar amfanin. Ya ce yadda aka tallafa wa noman shinkafa haka ya kamata a yi wa kasuwancin ridi.

Malam Muhammad daya daga cikin ’yan kasuwa masu sayar da ridin ya ce, ridi hanya ce ta samar da ingantaccen mai da kayan gina jiki da na more rayuwa da sauransu, musamman ga masu yin abubuwan gina jiki da masana’antu.

Ya ce ridi yana iya yin shekara bai yi komai ba matukar aka ajiye shi a wuri mai kyau.

A cibiyar kasuwancin ridi ta Babbar Kasuwar Sakkwato dillalan ridin sun ce, a yanzu suna sayo shi ne a kasuwannin garuruwan Gunjugu da Maigatari a Jihar Jigawa, sai Makarfi da Giwa a Kaduna da Talatar Mafara a Zamfara da Kasuwar Dange da Wurno a Sakkwato.

Buhun ridi a yanzu yana kai Naira dubu 34 zuwa dubu 40, kuma ana sayar da kwanonsa daya kan Naira 900.

A ta bakin Alhaji Umaru daya daga cikin dillalan da ke cibiyar, “A kowane mako ina tafiye-tafiye a wuraren da ake samun ridin amma yanzu ya yi wuya da kudinka Naira dubu 300 ba ka iya samun buhu 10.

Ya ce “Ridi ya yi tsada ne saboda masana’antu suna bukatarsa. A kasashe irin su China da Indiya suna amfani da shi wurin yin biskit da wasu kayan makulashe.”

Kan kalubalen da suke fuskanta kuwa ya ce, “Za ka iya sayen buhu in ka zo da kyar za ka iya samun rabin buhu, a wasu lokuta ma rabin buhun ya yi wuyar samu.”

Wata mai sayen ridi mai suna Fadimatu Muhammad mai shekara 40 a Unguwar Girabshi ta ce, tana sayen ridi ne ta fitar da mai cikinsa “Mukan soya mu nika, mu rika matsarsa har sai mun fitar da mai,” inji ta. Ta kara da cewar wadansu mutane suna cin sa, wadansu kuma suna shafa shi a fatar jikinsu, haka kuma wadansu suna gyaran gashin kai da shi domin gashi ya yi santsi.

Wani sanannen mai sayar da ridi a Kasuwar Sakkwato Alhaji Umaru ya ce su masu sayarwa ana mantawa da su wajen bayar da tallafi. Ya ce “Mun san inda muke sayen kayanmu mun san manoma to me ya sa ba a samu cikin abin da ake yi musu?”

“Idan aka samu matsalar masaya a Sakkwato sai mu dauki kayanmu zuwa garin Talatar Mafara mu sayar abin da ya tseratar da mu da yin hasara mai yawa,” inji Umaru

Ya bukaci tallafin gwamnati musamman ba su bashi mai sauki da za su kara habaka kasuwancinsu.