Farashin Shinkafa Ya Sauka A Najeriya

Farashin shansherar shinkafa na saukowa a kasuwannin hatsi a Najeriya.

Farashin Shinkafa Ya Sauka A Najeriya

Manoman shinkafa suna bugu, yayin da shanu suke cin raunonta

Wani bincike da Aminiya ta gudanar ya nuna cewa farashin shansherar shinkafa ya fara saukowa a kasuwannin hatsi a Najeriya.

Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da girbin shinkafa ’yar rani.

Masu kamfanin casar shinkafa dai shansherar suke saya sai su cashe ta su ɗure a buhuna su sayar wa masu buƙatar ci yau da kullum.

A shekaru uku da suka gabata, an sayar da buhun shansherar shinkafa mai nauyin kilogram 100 a tsakanin N9,000 zuwa N20,000.

Duk da cewa ba kuɗin bai ɗaya ake yi wa shansherar ba, farashin ta ya danganta ne da iri da ingancinta.

A watanni hudu na karshen shekarar 2023 zuwa bana, farashin shinkafar ya kai N55,000 zuwa N70,000.

Baya ga wasu abubuwa kamar farashin dizel da kudin sufuri, an danganta tsadarta kai tsaye da tsadar da tsabar shinkafa ta yi.

An gano cewa farashinta ya kai Naira dubu 80,000 kan buhu mai nauyin kilo 50 a  wasu jihohin Najeriya.

Sai dai wakilanmu sun gano cewa, a halin yanzu da ake ci gaba da girbin shinkafa ’yar rani, da kuma farfaɗowar darajar Naira, farashin ya fara faɗuwa.

Wakilinmu a Jihar Kebbi ya ce farashin ya yi kasa sosai a galibin yankunan da ake noman shinkafar.

Ya ce a ’yan watannin baya, an sayar da buhu mai nauyin kilo 100 a kasuwannin shinkafa daban-daban na jihar a kan N50,000 zuwa N55,000.

Amma a kasuwannin Aljanari da Suru, cibiyar noman shinkafa a Jihar Kebbi, yanzu ana sayarwa a kan Naira 43,000 zuwa Naira 45,000.

Haka kuma ana sayar da ita a tsakanin Naira 42,000 zuwa Naira dubu 45,000 a yankin Dakingari, maimakon yadda ta kai Naira 50,000 zuwa N56,000 kafin yanzu.

Wani mai harkar shinkafa a kasuwar Ambursa, Abubakar Sa’adu, ya shaida wa Aminiya cewa a halin yanzu farashin shinkafa mai ɓuntu na faduwa sosai a kasuwannin jihar.

“Ya danganta da ingancinta, har N37,000 ana sayarwa yanzu a wasu wuraren.”

Wani dan kasuwan shinkafa a babbar kasuwar Kamba, Suleiman Gado, ya ce ana sa ran farashin fadi zai cigaba da raguwa nan da ’yan watanni masu zuwa.

“Idan bude iyakar Najeriya da Jamhuriyar Nijar ta tabbata, ’yan kasuwa daga can suna shigo da ita, farashin zai kara sauka sosai.

“ Farashin yana kasa kusan kowane mako a cikin wata dayan nan da ya gabata zuwa yanzu,”

Aliyu Zauro wani manomin shinkafa a Birnin Kebbi, ya bayyana wa wakikinmu cewa noman rani da aka yi ne ya haifar da saukin shinkafar.

A Jihar Neja ma dai shansherar shinkafar ta sauka ainun, inda wakilinmu ya ruwaito cewa, farashin ya fadi a cikin ’yan makonnin da suka gabata.

Manoma da dillalan da suka yi magana sun ce a yanzu farashin ya tashi daga N39,000 zuwa N42,000 na buhun 100kg na paddy.

A Kasuwar Larabar Tambarin Gwani da ke Dutse babban birnin Jihar Jigawa, an sayar da buhun Fadi a kan Naira 55,000 a ranar Laraba, 17 ga watan Afrilu, inda aka sayar da buhun shinkafa daga Naira 60,000 a makonnin da suka gabata.

Masu siyar da Fadi a kasuwar sun danganta faɗuwar farashin da “yawan fadin aka samu” a kasuwar.

Aminiya ta lura cewa kasuwar Larabar Tambarin Gwani babbar kasuwar hatsi ce a Dutse, mutane daga sassa daban-daban na kasar nan ke zuwa.

Hakazalika, a jihar Taraba, farashin Fadi yana raguwa saboda buhu mai nauyin kilogiram 100, wanda aka sayar da shi kan Naira 50,000 a makon jiya, ya sauka zuwa Naira 40,000 a makon nan.

Wani dila a kasuwar Mutum Biyu Musa Kamal ya ce abubuwa biyu ne suka haddasa faduwar farashin.

Dalili na farko shine “Wasu manoman sun yanke shawarar sayar da ita ne domin su samu kudin noman damina, biyo bayan karatowar damina a jihar da wuri.

Na biyu kuma shine “an samu yawan Fadi a kasuwa, kuma babu masu saya da yawa”.