Farashin shinkafar gida ya sauka a Kebbi
Farashin shinkafar gida ya fara sauka a wasu manyan kasuwanni a Jihar Kebbi, kamar yadda bincike da wakilinmu ya yi a kasuwannin Bagudo, Tungar Giwa, dakingri, Kamba da Zuru da kuma Bunza da sauran manyan kasuwannin jihar Kebbi. Mudun shinkafa wanda a da ake sayar da shi a kan Naira 450 da kuma Naira 500 […]

Farashin shinkafar gida ya fara sauka a wasu manyan kasuwanni a Jihar Kebbi, kamar yadda bincike da wakilinmu ya yi a kasuwannin Bagudo, Tungar Giwa, dakingri, Kamba da Zuru da kuma Bunza da sauran manyan kasuwannin jihar Kebbi.
Mudun shinkafa wanda a da ake sayar da shi a kan Naira 450 da kuma Naira 500 a makonni biyu zuwa uku da suka wuce, yanzu ana sayarwa tsakanin Naira 250 da kuma Maira 280. Haka nan ma buhun shinkafar gida wanda ake sayarwa tsakanin Naira dubu 12 da 12, 500 a tsakanin mako biyu zuwa uku, yanzu ana sayarwa tsakanin Naira 8,000 da kuma Naira 8,500.
Shugaban masu sayar da shinkafa a kasuwar Tungar Giwa, Alhaji Rabi’u Maishinkafa ya ce dalilin da ya kawo faduwar farashin shinkafa ya danganta ne a kan yadda aka kawo ta a kasuwanni da yawa. Kamar yadda ya ce, kyakkyawar daminar da manoma suka samu a cikin ikon Allah hakan ya ba da gudunmuwa wajen kawo ta kasuwanni da yawa. Ya kara da cewa farashin zai iya kara faduwa kasa, idan aka ci gaba da shigowa da ita kasuwa da yawa.
Haka kuma farashin shinkafar waje ya fadi kasa, domin kuwa mudu daya da ake sayarwa Naira 650, yanzu ya koma Naira 450. Haka kuma buhu mai nauyin kilogiram 50 wanda ake sayarwa Naira 14,000 yanzu ya koma Naira 12,000.