Farashin tumatir ya fado a Kano bayan ya yi tashin gwauron zabi
A karon farko a jihar Kano, farashin tumatir ya fadi wanwar kwanaki kadan bayan annobar rubewa ta sanya ya yi tashin gwaron zabi. Wannan dai na zuwa ne yayin da ya rage kwana daya ko biyu kafin ranar Sallah Karama, wanda a baya lokaci ne da farashin kayan miya da kayan masarufi ke tashi. Gidauniya […]
A karon farko a jihar Kano, farashin tumatir ya fadi wanwar kwanaki kadan bayan annobar rubewa ta sanya ya yi tashin gwaron zabi.
Wannan dai na zuwa ne yayin da ya rage kwana daya ko biyu kafin ranar Sallah Karama, wanda a baya lokaci ne da farashin kayan miya da kayan masarufi ke tashi.
- Gidauniya Ta Dinka wa Marayu 103 Kayan Sallah A Gombe
- Matashin da ya je Masallacin Kudus a kafa daga Faransa
Aminiya ta yi tattaki zuwa Kasuwar ’Yan Kaba wacce ita ce cibiyar hada-hadar kayan miya a Jihar Kano, inda muka gano cewa farashin kayan miya musamman tumatir ya yi kasa sosai fiye da makonni uku da suka gabata.
Idan ba a manta ba dai a kwanakin bayan ne Kungiyar Manoman Tumatir reshen jihar kano (TOGAN) ta bayyana cewa, cutar da ke yi wa tumatir illa ta sake afkawa a wasu gonaki a jihar.
A lokacin, shugaban kungiyar reshen jihar, Alhaji Sani Danladi Yadakwari, ya bayyana wa manema labarai cewa, idan ba a yi hankali ba, hakan zai sanya a samu karancinsa da kuma tsadarsa.
Malam Ibrahim, wani matashi ne da ke sayar da kayan miya a kasuwar ta ’Yankaba ya ce baya ga wancan ibtila’i da ya afkawa tumatir a jihar, tsananin zafin da ake yi ya bayar da gudummawa wajen sanya tsadarsa a kasuwa.
“Dalili ba tumatir din damina ba ne ko sanyi, dan rani ne, to idan aka yi rana sosai, na gonar za ki ga manyan sun mutu, tushen ya mutu shi ma.
“Saboda haka sai karancinsa ya sanya ya yi tsada; Amma yanzu farashin ya canja ya ma fi sauki fiye da a baya.
“Yanzu kin ga kwandon N17,000, da N15,000 ne, da karami N5,000, kwanonsa kuma N700 ne zuwa N500, amma kwanaki kuwa kin ga ai kwandon ya fara ne daga N22,000 zuwa N20,000.”
Babu ciniki —’Yan Kasuwa
Malam Ibrahim ya ce, “A sallar bana kasuwa babu ciniki sai dan abin da ba za a rasa ba, saboda sallah ta matso amma ba mu san inda aka saka gaba ba.
“Bara war haka kasuwar nan a cike take ana ta hada-hada amma yanzu watakila don babu kudi a hannun mutane ne shi ya sa ba kowa ke zuwa nan ba.
“Wadandamuka saba suna zuwa saye da yawa yanzu sun koma sayen kadan.
“Kin ga waccan sallar a irin wannan lokacin daga safe zuwa yamma na sayar da kayan miya na N100,000 amma yau ko na N30,000 ban sayar ba.”