Farashin tumatir ya sauko a kasuwannin Jihar Legas
Ga alamu farashin tumatiri ya sassauto a kasuwan-nin daban-daban da ake sayar da kayan gwari a Jihar Legas. Binciken Aminiya da ta gudanar a farkon makon nan, ya gano cewa kwandon tumatiri da ake sayar da shi naira dubu 30 kacal, a yanzu ana sayar da shi kasa da Naira dubu ishirin da bakwai.Dillalan tumatir […]
Ga alamu farashin tumatiri ya sassauto a kasuwan-nin daban-daban da ake sayar da kayan gwari a Jihar Legas.
Binciken Aminiya da ta gudanar a farkon makon nan, ya gano cewa kwandon tumatiri da ake sayar da shi naira dubu 30 kacal, a yanzu ana sayar da shi kasa da Naira dubu ishirin da bakwai.
Dillalan tumatir a kasuwannin daban-daban da ke jihar sun bayyana cewa farashin ya ragu ne saboda shigowar sabon tumatir daga sassa da dama na kasar nan.
Sakataren dillalan tumatir da ke kasuwar Mil 12, Alhaji Lawan Bilya Adam, ya bayyana cewa tumarin zai ci gaba da saukowa har sai farashinsa ya daidaita a kasuwa ta yadda zai yi arha.
Ya ce, “Babu shakka za mu iya cewa an dan samu sauki a farashin. A baya muna sayar da kwando naira dubu 30, amma yanzu ana sayar da kwando naira dubu takwas har kasa da haka. Kuma ba komai ba ne ya janyo haka ba illa shigowar sabon tumatir kasuwa. Yanzu akwai tumatir dan Jos da dan Kaduna. Hakazalika, an kawo tumatirin jihohin Yarabawa.”
Ya ci gaba da cewa, “Muna sa ran samun tumatiri daga kasar Ghana kwanannan. Da ma abin da ya janyo tsadar tumatirin shi ne karancinsa a kasuwa, amma yanzu da sabo ya fara zuwa dole ya sauko. Saboda haka muna sa ran nan da dan lokaci kadan farashinsa zai sauko ya daidaita a kasuwa.”
Shi ma da yake karin bayani, dillalin tumatir a kasuwar Akeson, Alhaji Muktar ya bayyana cewa lamarin haka yake a kasuwarsu.
“Mu ma a nan kasuwar mu farashin ya dan sauko daga naira dubu 30 zuwa naira dubu 27 har ma kasa da haka, amma kuma muna sa ran nan da dan lokaci zai yawaita a kasuwa kuma farashinsa zai kara sauko. Ba tare da wani bata lokaci ba. Duk lokacin da tumatirin wasu jihohi ya fara zuwa da na kasashen wajen to dole farashinsa ya sauko kasa dama haka kayan gwari yake, yau farashinsa ya hau gobe farashinsa ya sauko,” inji shi.