Farfado da Kamfanin Tumatir na Gombe zai samar da ci gaba – Shugaban Masu Tumatir
Wakilin Shugaban masu sayar da kayan gwari na Jihar Gombe, Alhaji Sani Waya, ya yi kira ga gwamnati ga bukatar da ake da farfado da kamfanin sarrafa tumaturin gwangwami da Mangwaro dake garin Kumo na karamar Hukumar Akko. Shugaban ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da Aminiya a kasuwar gwarin dake […]
Wakilin Shugaban masu sayar da kayan gwari na Jihar Gombe, Alhaji Sani Waya, ya yi kira ga gwamnati ga bukatar da ake da farfado da kamfanin sarrafa tumaturin gwangwami da Mangwaro dake garin Kumo na karamar Hukumar Akko. Shugaban ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da Aminiya a kasuwar gwarin dake Gombe.
Ya ce a halin yanzu an fara fadada noman kayan lambu a jihar nan, babu shakka yin hakan zai kara samar da ci gaba da kuma sarrafa shi a leda da gwangwamaye wanda kuma zai samar da aikin yi ga matasa da kuma kara samun kudaden shiga cikin sauki.
Haka kuma ya ce baya ga yadda ake sayen kayan lambun anan cikin gida, suna kuma fitar da kayan zuwa dukkan jihohin Najeriya, wadda kuma kayan Gombe shi ne mafi kyau a kasuwannin da muke kai kayayyakinmu, domin ko ana cin kasuwa, da zarar kayan Gombe ya iso, to sai ka ga an tattara an koma kansa.
Haka zalika ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jiha da cewa su bai wa sashen noma karin kudi kimanin kashi 30 cikin 100 na kasafin kudin da ake da shi, idan aka yi haka za ka ga yadda harkar noma musammam na kayan gwari zai inganta.
Da yake bayyana halin rahusar da kayan lambun ya yi, wadda yake sanya farin ciki a fuskar kwastomomin dake shigowa kasuwar, Alhaji Waya, ya ce yanzu an samu saukin kayan da kuma wadatuwarsa ba kamar a ’yan kwanakin baya ba.
Ya ce yanzu kayan gwari irin Tattasai da Tumatur da ma sauransu da ake nomawa suna karuwa, kuma an samu wadatarsa. Wakilin ’yan gwarin ya ce a baya ana sayar da kwandon Tumaturi akan kudi naira dubu 18, amma yanzu ya dawo dubu biyar ko hudu, har ma kasa da haka wani lokacin.
Tattasai kuma a baya ana sayar da Solon buhun shi dubu 17, amma yanzu bai wuce dubu bakwai zuwa dubu shida ba. Ita kuwa albasa hawa biyu ake da ita, akwai ’yar Gaidam wacce ake sayar wa dubu 11 zuwa 12, akwai kuma ’yar Zariya wacce ake sayarwa dubu bakwai.
Amma a baya ba ta kai haka ba, saboda karancin ta ne ita kuma yanzu shi yasa ta dan yi tsada. Duk da karuwar da manoman suka yi, kuma aka samu wadatuwar kayan gwarin babu tallafin gwamnati ga manoma a ciki kamar na samar musu da bashi marar ruwa wanda suka nema a baya, da gwamnati ta shigo ta taimaka musu da babu lokacin da za a ce kayan gwari ya yanke a jihar Gombe.