Farfado da martabar Arewa ne dalilin kafa kungiyar NRI – Alhaji Abubakar

Jagoran kungiyar Farfado da Martabar Arewa wato (Northern Reformation Initiatibe) wato NRI, Alhaji  Abubakar Adam ya ce sun kafa kungiyar ne domin yin aiki wajen farfado da martabar yankin Arewacin tare da kyautata dangantaka tsakanin yankin da sauran sassa na kasar nan.Yayi wannan tsokaci ne a zantawarsa da wakilinmu, ya ce “lokaci ya yi da […]

Farfado da martabar Arewa ne dalilin kafa kungiyar NRI – Alhaji Abubakar
Farfado da martabar Arewa ne dalilin kafa kungiyar NRI – Alhaji Abubakar

Jagoran kungiyar Farfado da Martabar Arewa wato (Northern Reformation Initiatibe) wato NRI, Alhaji  Abubakar Adam ya ce sun kafa kungiyar ne domin yin aiki wajen farfado da martabar yankin Arewacin tare da kyautata dangantaka tsakanin yankin da sauran sassa na kasar nan.
Yayi wannan tsokaci ne a zantawarsa da wakilinmu, ya ce “lokaci ya yi da za a samar da wani tsari wanda zai yi  dawo da martabar yankin arewacin kasar nan tareda bunkasa hadin kai tsakanin yankin da sauran sassa na fadin kasar nan.”
Daga nan ya nunar da cewa sun dade suna kokarin hada wannan kungiyar. Har ila yau, sun kammala  tuntuba tsakanin jihohin da ke yankin, wanda ya zuwa yanzu, ya ce “kusan dukkanin jihohin kasar nan suna cikin wannan tafiya.”
Hakazalika, ya ba da tabbacin cewa za ta kasance wata hanya ta kyautata dangantaka tsakanin Arewacin kasar nan da sauran yankuna domin a cewarsa,  wajibi ne Najeriya ta kasance kasa daya al’umma daya.
Dangane da irin shirye-shiryen da kungiyar take yi na fara aikinta, Alhaji Abubakar ya tabbatar da cewa  kungiyar za ta  rika fitar da manufofinta da tsare-tsaren yadda tafiyar za ta kasance.