Farfado da soyayya cikin rayuwar ma’aurata (5)

Assalamu alaikum. Barkanmu da sake haduwa a cikin wannan fili da fatan Allah Ya amfanar da mu dukan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga ci gaban bayani kan abubuwan da ke suke nakasa so da kauna tsakanin ma’aurata: Sululu kasau din soyayyar auratayya Na kira su da sululu kasau saboda raunuka ne na […]

Farfado da soyayya cikin rayuwar ma’aurata (5)
Farfado da soyayya cikin rayuwar ma’aurata (5)

Assalamu alaikum. Barkanmu da sake haduwa a cikin wannan fili da fatan Allah Ya amfanar da mu dukan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga ci gaban bayani kan abubuwan da ke suke nakasa so da kauna tsakanin ma’aurata:

Sululu kasau din soyayyar auratayya

Na kira su da sululu kasau saboda raunuka ne na zamantakewar rayuwar aure, wadanda a boye suke, kuma da yawa mutane suna ganin ba su haifar da wata illa cikin rayuwar aure, amma a hakikanin gaskiya ba abu mai kashe soyayyar aure da kashe auren gaba daya irin wadannan abubuwa. Kuma a hankali suke cinye soyayyar cikin aure ba tare da an ankara ba sai a wayi gari auren na tangal-tangal.

1.    Rashin son Allah

Rauni na farko shi ne halin ko-in-kula da kiwar wadansu ma’aurata na rashin cakuda son Allah cikin soyayyarsu, da rashin sa Allah sama da komai a cikin sha’anin zamantakewar aurensu. Domin in ana kula da son Allah cikin zuciya, to zai kasance ko me mutum zai yi sai ya kawo Allah da tunanin yanayin wannan aiki a addinance. In ma’aurata na kula da soyayyar Allah cikin zuciyarsu, to Allah zai kular musu da soyayyar da ke tsakaninsu, ba za ta bushe ta rame ko ta mutu gaba daya ba! Soyayyar Allah ita za ta kara tabbatar da rayar da soyayyar da ke tsakaninsu.

Maganin haka shi ne ma’aurata su lullube zuciyarsu, jikinsu, ayyukansu da rayuwar aurensu da son Allah mai yawa, mai tsananin kauri kuma mai tsananin karfi, wannan zai sa kowace irin matsala za ta shigo musu to sai dai ta kare su da alheri ba ta rage su ba. A dage wajen bin dokokin Allah gaba dayansu, kada mutum ya ce ai na yi iyakar yi na, iyakar mumini wajen bin dokokin Allah ba su da iyaka, domin duk dokar da Allah Ya sa wa dan Adam, to kuwa Ya ba shi ikon bin ta dari bisa dari. Kuma kada a gajiya da neman ilimin sanin abin da ya dace da abin da bai dace ba, don a kara kiyaye dokokin Allah (SWT).

Rashin yin addu’a

Akwai sakacin rashin yin addu’a game da soyayya a tsakanin ma’aurata. Da yawan ma’aurata sukan mance su rika rokon Allah da Ya dauwamar da soyayyarsu a cikin zukatansu, ya kasance al’amura da rayuwa mai kyau da mara kyau in sun taho, sai dai su kara wa soyayyar tasu karfi ba su raunatar da ita ba.

Maganin haka shi ne sai a binciki Alkur’ani Mai girma da kyawawan sunnoni da dabi’un Manzon Allah (SAW), don a samu kyawawan addu’o’i na karin soyayya da jin dadin zamantakewa tsakanin ma’aurata. Allah Ya tanadar mana kowane irin jin dadin rayuwar duniya cikin Littafinsa mai cike da alherai da Sunnar ManzonSa (SAW) amma sai ya kasance muna yi musu rikon sakainar kashi, ba ma amfani da su wajen kaucewa ko warware matsalolin rayuwarmu da zamantakewarmu.

Ga wasu daga cikin irin wadannan kyawawan addu’o’i, sai a dage a rika yi koda cikin sujadar karshen kowace Sallah ce, da fatan Allah Ya sa mu dace da alheran da ke cikin son Allah da bin dokokinSa, amin.

1.    Rabbana, hablana, min azwajina, wa zurriyatina, kurrata a’ayuni waj’alna lil muttakina imama.

2.    Allahumma inni as’aluka an taj’ala hubbi, fi kalbi zauji, wa yarani kama yara jahahu fi munadirati fi kulli wakti; fi aunihi hadiran au safaran, Ya Rabbil alamin; ajib du’a’i, wagfir li zunubi, waj’al fi kulli amri inda zauji mashkuran fi baitihi min sairihi ma wajadtani indahu.

Addu’a ta biyu domin uwargida na kawo ta, ta rika yi cikin kowace sujadar karshen kowace Sallarta don dauwamar da soyayyarta cikin zuciyar maigida, amma maigidan da ya ji yana bukatar mallake uwargidansa, to inda aka sa zauji (wato mijina) sai ya sa zaujatiy (matata) da fatan Allah Ya amsa mana addu’o’in mu, amin.

Sai mako na gaba insha Allah. Da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a koyaushe, amin.