Farfado da soyayya cikin rayuwar ma’aurata (6)

Assalamu alaikum, barkanmu da sake haduwa a cikin wannan fili. Da fatar Allah Ya amfanar da mu dukan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga ci gaban bayani kan abubuwan da ke suke nakasa so da kauna a tsakanin ma’aurata:   Tsinkewar hanyar sadarwa In ya kasance ma’aurata suna zaune lafiya, ba mai jin […]

Farfado da soyayya cikin rayuwar ma’aurata (6)
Farfado da soyayya cikin rayuwar ma’aurata (6)

Assalamu alaikum, barkanmu da sake haduwa a cikin wannan fili. Da fatar Allah Ya amfanar da mu dukan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga ci gaban bayani kan abubuwan da ke suke nakasa so da kauna a tsakanin ma’aurata:

 

  1. Tsinkewar hanyar sadarwa

In ya kasance ma’aurata suna zaune lafiya, ba mai jin kansu, amma sai ya kasance kuma ba wata cikakkiyar sadarwa a tsakaninsu, kowa bai san abin da dan uwansa yake ciki ba, to wannan zai haifar da babban gibi cikin rayuwar aurensu. Wani lokaci rashin sadarwa tsakanin ma’auratan mai asali ce, da ita suka fara rayuwar aurensu, wani kuma wani abu ne kan faru cikin zamantakewar rayuwar auren sai ta tsinke hanyar sadarwa a tsakanin ma’aurata.

Misali: Maigida in ya dawo, uwargida ta yi masa sannu da zuwa ta kawo masa abinci, in ya ci ya kunna rediyo ko talabijin yana saurare; koda ya ga gidan fes-fes da shi bai san ya yi mata sannu, godiya ko ya yaba da kokarinta ba. Haka ita ma ba batun ta tambaye shi yanayin fitarsa ta ranar, ko ta yi masa godiya ta yaba da kokarin da yake yi. Ba a zama a yi ’yar hira ta wasa da dariya, ba su gaya wa juna damuwarsu da sirrikansu. Da yawan ma’aurata yadda wadansu ’yan uwansu ko kawayensu suka san sirrinsu, wadanda suke aure ba su san haka ba. In wata matsala ce da ta danganci ibadar aure ba a iya fada wa juna, akwai da yawan matan da ibadar aure ta kasance kamar azaba a gare su, zafi suke ji sosai, amma ba sa taba bari maigida ya gane, sai dai su yi ta daurewa suna shan azaba shekara da shekaru. Akwai kuma matan da ba su samun gamsuwar ibadar aure, amma ba sa iya fada wa mazan, ko su nuna abu kaza da abu kaza suke so lokacin ibadar aure. Wani lokacin ma har karyar nuna gamsuwar suke yi don dai kada mazan su gane; akwai wadda tana jin tsananin bukatar maigida, amma sai dai ta hadiye abinta ba ta iya nuna masa, sai dai in shi ne ya neme ta. Haka mazan ma, wani za ka ga akwai wani abu da yake so matarsa ta rika yi masa, ba ta yi din kuma bai iya gaya mata, da sauran misalai da yawa.

Irin wannan duk na faruwa ne saboada rashin sahihiyar kafar sadarwa a tsakanin ma’aurata; matsaloli da yawa za su kau daga cikin rayuwar aure in dai akwai sahihiyar kafar sadarwa a tsakanin ma’aurata, domin haka shi zai haifar da cikakkiyar fahimtar juna a tsakanin ma’aurata. To in kuwa aka samu fahimtar juna, to rigakafi ne na kowace irin matsala da ka iya kunno kai cikin rayuwar aure.

Maganin haka shi ne, maigida ya sani shi ne ja gaba kuma jagoran gidansa, shi ke shimfida duk dokar da ya so cikin gidansa, saboda haka shi ya fi dacewa ya tabbatar da tabbatuwar hanyar sadarwa tsakaninsa da iyalansa, in kuma ta tsinke, shi ya kamata ya sake kulla sabuwar hanyar sadarwar.

Ma’auratan da ke da irin wannan matsala ta rashin sahihiyar sadarwa a tsakaninsu, yana da kyau su magance ta tun kafin ta yi nisan da maganceta na iya zama sanadiyyar bullar wata barakar kuma. Duk wata damuwa ko wani hali da daya ke ciki sai ya daure ya rika sanar da dayan, ta haka sai su taru su nemi maganin matsalar. In ma akwai shakkar samun mummunar fahimta daga wanda ake auren, sai mutum ya zauna, ya yi nazarin matsalar da nazarin abokin zamansa sannan ya yi nazarin hanya mafi dacewa ta sanar da shi wannan maganar ta yadda zai fahimta kyakykyawar fahimta.

Sannan yana da matukar alfanu ga dukan ma’aurata, hatta wadanda ke da kyakykyawar hanyar sadarwa a tsakaninsu, ya kasance sun sanya wata rana, koda karshen kowane wata ne domin su zauna zama na musamman don tuntubar juna da nufin sanin matsalolin da daya ko dukan iyalan ke cike don a samo hanyar magance su. Maigida shi ne zai jagoranci wannan zaman tattaunawa kuma har yaran gida yana da kyau a shigar da su ciki, kuma a ba kowa dama ya tofa albarkacin bakinsa don gano sababbin hanyoyin da za a bi don ciyar da gidan gaba da karin jin dadin zamantakewa da soyayya. Mu lura, ko manyan kamfanoni da ma’aikatu ba su ci gaba sai da irin wannan zaman tuntuba da tattaunawa, to kuwa ba kamfanin da ya kai kamfanin gida da iyali, komai da komai na mutum a nan yake; hatta hanyar samun tsira ranar gobe Kiyama. Da fatan Allah Ya sa mu dace amin.

  1. Rashin sadaukarwa

Aure wani abu ne da ya kasance da an yi shi, to ma’aurata sun zama daya ta kowace fuska, amma auren yanzu na kowa kansa ya sani ne, ba na a taru a taimaki juna, a rufa wa juna asiri ba ne. Wannan ware kai da ma’aurata ke yi na rage rahama da jinkai a cikin auratayyarsu, yana cire dumin soyayya, auren ya kasance ya zama a sandare.

Maganin haka shi ne ma’aurata su cire tsananin son kai daga cikin rayuwar aurensu, uwargida ta sa bukatun maigida sama da nata, haka shi ma maigidan. In sun yi haka za su ga aurensu na ci gaba, kuma soyayyarsu na dada karfi, da fatan Allah Ya sanya tsananin sadaukarwa a zuciyar dukan ma’aurata domin samun ci gaba da karuwar soyayya a tsakanin su, amin.

 

Sai mako na gaba in sha Allah, da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a koyaushe, amin.