Farfado da soyayya cikin rayuwar ma’aurata (9)
Assalamu alaikum. Barkanmu da sake haduwa a cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga karashen bayani kan Hadisin Ummu Zar’in: Siffofin maigidan da kowace uwargida ke ki Za mu yi amfani da karashen Hadisin Ummu Zar’in don yin bayani a kan siffofi da […]
Assalamu alaikum. Barkanmu da sake haduwa a cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga karashen bayani kan Hadisin Ummu Zar’in:
Siffofin maigidan da kowace uwargida ke ki
Za mu yi amfani da karashen Hadisin Ummu Zar’in don yin bayani a kan siffofi da halayen magidanta da kowace uwargida ke kyama. Matan da ba su yabi mazansu ba a Hadisin Ummu Zar’in su biyar ne, ta 1, 2, 3, 6, da kuma ta 7
1. Mace ta 1: “Mijina kamar naman ramammen rakumi ne wanda babu tsoka a jiki, wanda aka dora a saman kololuwar tsauni mai wahalar hawa; ga shi tsaunin mai wuyar hawa sosai ballantana a hau a dauko, shi kuma naman bai da kaurin da zai kwadaitar da mutum balle ya daure wahalar dauko shi.”
Yadda ta kwatanta shi da nama mafi karantar daraja cikin dabbobin ni’ima ya nuna mijinta mai mummunan hali ne; mai rowa mai girman kai kuma mai wuyar sha’ani; kwata-kwata ba ta jin dadin zama da shi, sannan duk wani hakuri da sadaukarwar da za ta yi game da shi, to ba wani sakamakon kyautatawa daga gare shi.
2. Mace ta 2: “Mijina…! Ai ba ni iya cewa komai game da shi; ina jin tsoron, in har zan yi maganarsa, to ba zan rage komai ba na daga munanan halayensa, wanda hakan zai sa ku daina ganin kimarsa.”
Yadda ta siffanta mijinta ya nuna munanan halayensa sun yi yawa matuka har tana tsoron ta fada don kada sauran matan su daina ganin kimarsa; kuma ba ta son ta fara fada ta kasa karasawa saboda yawansu; kuma ba ta son ta rage komai daga cikin munanan halayensa.
3. Mace ta 3: “Mijina, mai tsananin tsawo ne kuma mai tsananin siranta ne, in na yi magana a sake ni; ina na yi shiru kuma a mayar da ni gefe ba a yi da ni.”
Wato tana nufin ba ta inda mijinta yake burge ta: halinsa bai burge ta ba saboda in ya yi mata laifi ba ta da damar tankawa, domin in ta tanka tabbas zai sake ta, in kuma ta yi shiru sai ya share ta ya daina kula ta; haka kuma siffarsa ma ba ta burge ta ba.
4. Mace ta 6: “Mijina, in zai ci abinci, zai cinye duka ba tare da ya rage komai ba; haka ma abin sha zai kwankwade shi duka; sannan in ya kwanta zai yi ta barci har gari waye; ba ya kai hannunsa gare ni ya ji yaya nake, in ina cikin rashin lafiya.”
Bayaninta ya nuna mijinta mai hadama ne kuma marowaci, komai ya samu cikinsa kawai ya sani; kuma bai damu da hakkin ibadar aure ba, sannan bai kula da yanayin da uwargidansa take ciki ba, in tana cikin yanayin rashin lafiya ko bacin rai, ko sannu bai ce mata balle ya tausaya mata.
• Mace ta 7: “Mijina, rago ne, mai yawan maula; ga shi azzalumi, mai yawan zaluntar duk wanda yake tare da shi; ga shi wawa, mai sakin baki; kowace irin cuta da da namiji ke da ita shi ma yana da ita; kullum aka wayi gari, kodai ya buge ki ya fasa miki kai, ko ya hankade ki ki fadi ki yi targade ko ya hada miki duka biyun”
Wannan miji shi ya fi duk sauran tsananin rashin kyautatawa da kuma tarin munanan halaye; ta bayyana shi mutum mai yawan roko da maula; yau in ya je gun wannan dan uwa gobe ya je gun wancan aboki. Sannan soko ne shi don bai iya magana ba, komai ya fito bakinsa cabawa yake; sannan ta ce shi azzalumi ne kuma ya tara dukan cututtukan halayya da mu’amala na da namiji yake da su.
Darussa:
• Za mu fahimci cewa daga cikin dukan wadannan maza ba wanda bayani ya nuna shi mawadaci ne; ta yiwu daga cikinsu akwai masu wadatar dukiya, amma rashin tausayawa da kyautata mu’amala ya sa wadatar dukiyarsu ba ta yi tasirin komai ba ga matan nasu. Don haka ba su ba ta muhimmanci cikin bayanan nasu; wannan ya nuna mana cewa kyakkyawar mu’amala ita ce babbar daular da miji zai iya ba matarsa!
Sai mako na gaba insha Allah, da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarsa a koyaushe, amin.