Farfado da tattalin arzikin Najeriya
A zamuna daban-daban an sha shirya tsare-tsare da za a gwada don kasar nan ta ci gaba. A yayin da burin shugabanni shi ne kasar ta zama cikin kasashe 20 masu karfin tattalin arziki a shekara ta 2020. Masana sun nuna cewa tattalin arzikin kasar zai iya habaka idan aka yi sa’ar samun shugaban da […]
A zamuna daban-daban an sha shirya tsare-tsare da za a gwada don kasar nan ta ci gaba. A yayin da burin shugabanni shi ne kasar ta zama cikin kasashe 20 masu karfin tattalin arziki a shekara ta 2020. Masana sun nuna cewa tattalin arzikin kasar zai iya habaka idan aka yi sa’ar samun shugaban da zai tafiyar da kasar tare da amfani da arzikin kasar wajen raya ‘yan kasa. Hakan ya sa aka kafa tsarin Sure-P da shirin nan You-Win da gwamnatin shugaba Jonathan ta kafa a wani shirin zamanatar da Nijeriya!
Hakika Nijeriya na da damar taka rawar gani a tattalin arzikin duniya hakan ya sa aka jera ta a kasashen da ake gani nan gaba za su yi tasari watau MINT, Meziko, Indonesiya, Najeriya da Turkiya. Kamar yadda kwararren masanin nan na tattalin arziki Jim O’neill ya yi hasashen tasowar kasashen da ya wa lakabi da BRIC watau Barazil da Russia da Indiya da Caina. Daga bisani aka kara, inda suka zama BRICS bayan an kara Afrika ta Kudu. Ganin suna da abubuwan da ake bukata kasa ta bunkasa watau ma’adanai, masana’antu ko makamashi da yawan jama’a.
Manazarta sun gane akwai garabasa a nahiyar Afirka, musamman ganin yawan mabukata. A haka kafa kamfanoni ko kai kayan Caina na cinye ciniki. Hakan na kara nuna mana idan attajirai sun zuba jari, kamai zai sauya! Domin kowa a duniya ya san yadda ‘yan Najeriya suke da kudi a kasashen waje, sannan ga irin kasuwar da ke akwai a Najeiya ta kayan abinci, sumunti da sauran kayan gine-gine da tufafi da sauransu. Dadin dadawa akwai kasawu a Najeriya, kusan duk abin da aka kai daga kasashen ketare sai an sayar, domin babu kamfanoni, sannan ba a inganta abubuwan da ake iya sarrafawa a kasar.
Tattalin arziki na tafe tare da siyasar kasa, shi yasa idan aka samu tsayayyen tsarin tafiyarwa a siyasance akan sami bunkasar tattalin arziki ta fuskar wadata, ba yaudara ba, amma idan ana fada ba a cikawa, zaku iske mutane suna fama da talauci da maula, sai ka ga a irin wadannan al’umomin ne ‘yan siyasa ke shimfida tabarmar fadanci!
Duk da cewa cin hanci da rashawa kan zama abin da ya hana kasar nan tashi tsaye, dole sai an kashe wannan cutar ta hanyar yakar ta kafin ta cinye jikin, domin wasu manzartan na ganin kasar ta hau hanyar zuwa makabarta, domin komai ya tsaya, ko ma abin da ke aiki na neman tsayawa!
Tabbas kowame tsuntsu kukan gidansu yake yi, dole a fara da ‘yan siyasa. Shugabanni su amince zasu yi adalci a bisa mukamai ko amanar da ke hannunsu, su nuna haka a zahiri, domin idan aka gyara saman dole kasa ta gyaru!
Sannan a gyara makarantu, ba wai a tsaya kan gini ko kwaskwarima ba, ko rubuta suna a jikin bango ko kwanon rufi, a kawo kayan aiki, a kawo karshen yaji aiki a makarantu, domin a kasar nan ba a bar malaman firamare da na sakandare ba wajen yajin aiki balle uwa uba jami’a. Ilimi na da matukar muhimmanci wajen ci gana kowace kasa, babu ci gaban da za a samu sai da ingantaccen ilimi.
A zamantar da asibtoci, a gina sababbi, a wadatasu da likitoci da kayan aiki, a kara daidaita albashin ma’aikata, tare da ba wadanda ba su da aikin yi hakkokinsu haka a kulla da tsofaffi masu fensho. Kai ko titunan kasar nan na bukatar a saitasu, wasu hanyoyin sun zama tarkunan mutuwa, yana da wuya motoci 50 su wuce ba tare da samun wasu sun yi hadari ba! A haka ya dace a mikar da hanyoyinmu a kulla da su a tabbatar da motocin haya da direbobi na kulla da rayuwar fasinjoji. Daga karshe idan aka bunkasa harkar masana’antu, aka raba kafa, aka rage dogaro da man fetur a matsayin hanyar samun kudin shiga, za a dauki ma’aikata kuma za a samu abin yi da zai rage yawan mabarnata da mabarata, musamamn idan aka bunkasa noma da kiwo, a gina gonakin zamani
Haka duk na bukatar tsayayyar wutar lantarki, wadda za ta ba dubbunan talakawa ayyukan yi a zama daya kamar masu walda da nika da aski da gidajen kallo da kwamfuta, tare da tada komadar kamfanoni. Yayin da haka zai zama sillar cin moriyar kimiyya da fasaha wadanda da su kadai za a raya tattalin arziki.
Masana tattalin sun tabbatar da akwai bambancin ci gaban tattalin arziki da ci gaban halin da mutane suke ciki, domin sau da yawa gwamnotoci kan gwada ci gaba da masana’antun da suke tashe ko dan abin da ba a rasawa a bangaren kudin shiga. Wasu matakan farfado da tattalin arziki a kasashe masu tasowa su ne kyankyashe masana’antu jarirai da daukar ma’aikata, domin ga rundunonin matasa nan a jibge ko’ina, sayen injuna, wadanda za su kai ga kafa kamfanoni a kasa. Turawa sun tabbatar da cewa Afirka kasuwar duniya ce!
kasa kamar Najeriya na da damar samun kudi ta hanyoyi da dama, amma a halin da ake ciki yanzu ko attajiran kan kara kashe tattalin ta hanyar rashin biyan haraji, musamman hamshakan, wadanda ake daga wa kafa, a tafi tare da ‘yan siyasa, su yi abin da suka ga dama a sunan sun kai kololuwa.
A halin yanzu Najeriya ta shiga wani yanayin da bata taba shiga ba a tarihin kafuwarta, ba wanda ya san hakan zai haifar da ci gaba ko kasar ta dauki hanyar fakat, ko za ta farfado daga gyangyadin da ta yi, ta dauki matsayinta a fagen kasashen duniya.
Buhari Daure
+2347035986444
Muryar Talaka
[email protected]