Farfadowar tattalin arziki: Mu gani a kasa
Editan Aminiya ka ba ni dama in yi tsokaci kan yadda za a tabbatar da amfanin bunkasar tattalin arzikinmu ga talakawan kasa. Mun yi farin ciki kuma mun yi murna da jin tattalin arzikin kasarmu ya samu tagomashi, to amman fa an ce ana biki gidan su kare ya ce mu gani a kasa, ko […]
Editan Aminiya ka ba ni dama in yi tsokaci kan yadda za a tabbatar da amfanin bunkasar tattalin arzikinmu ga talakawan kasa. Mun yi farin ciki kuma mun yi murna da jin tattalin arzikin kasarmu ya samu tagomashi, to amman fa an ce ana biki gidan su kare ya ce mu gani a kasa, ko shakka babu galibin talakawan Najeriya ba su san tattalin arzikin kasar mu ya samu tagomashi ba, domin har yanzun talakawa na kwana da yunwa, da tsadar rayuwar nan dai tana nan. Hakan ya sa talaka ke ganin kamar tattalin arzikin kasar mu bai samu tagomashi ba. Don haka ne nake kira ga Shugaba Buhari, shugaban da tun kafin ya hau mulki ake yi masa ikirari da shugaban talakawa, dattijo mai fada da cikawa, da ya yi wani tsarin da talakawan da ke a karkara ko in ce kauyuka za su amfani tattalin arzikin kasarmu da aka ce ya bunkasa, musamman kudin da Hukumar EFCC ke kwatowa daga hannun barayin gwamnati.
Daga Abba Sa’ad Mahuta, dan kungiyar Muryar Jama’a, reshen Jihar Katsina, 07062545272. [email protected].