Farfesa 5 da wasu malaman jami’a 5 sun rasu a yajin aiki —ASUU
Farfesoshi biyar na cikin malaman jami’a 10 da suka rasu a cikin yajin aikin ASUU
Malaman jami’a 10 ne suka rasu a jami’ar Calabar a sakamakon yajin aikin da su ke yi na kasa baki daya tun daga ranar 14 ga watan Fabrairu.
Shugaban ASUU reshen Jami’ar Kalaba, Dokta John Edor ya ce farfesoshi biyar na daga cikin malaman jami’ar da suka rasu a cikin yajin aiki..
- ASUU: Sam gwamnatin Buhari ba ta muntunta Ilimi – Sanusi
- Yajin aikin ASUU: Gwamnati ta umarci a gaggauta bude jami’o’i
Ya sanar da haka ne a ranar Laraba a sanarwar da ya bayyana cewa malaman jami’a da suka rasu a jihar su 10 ne ba 21 ba, kamar yadda a ke ya yadawa a kafofin yada labarai.
Sannnan kuma ya tabbar da labarin cewa malaman sun rasu ne a sanadiyyar yajin aikin da kungiyar ta ke yi, kuma ya jaddada cewa, ba za babu gudu, babu ja da baya kan matsayinsu.
“Muna sane da barazanar yunwa da kuma barazanar ummarni kotu, amma hakan ba za su sa mu karaya ba, har sai gwamnati ta yi abin da ya dace,” in ji shugaban ASUU na jami’ar.
A baya-bayan nan Gwamnati Tarayya ta bayar da ummarni ga shugabannin jami’oi da su bude jami’oin don kawo karshen yajin aikin malaman, sakamakon kin bin umaranin kotu, amma ta janye.