Farfesa Amina Bashir: Yadda na yi gwagwarmayar shekara 30 ina koyarwa
Farfesa Amina Abubakar Bashir ta shafe shekara 30 tana koyar da Turanci a Jami’ar Maiduguri, ta rike mukamai da yawa a jami’ar. Ta yi bayanin yadda ta yi gwagwarmayar neman ilimi da kuma koyarwa, da yadda ta hada lura da iyali da kuma koyarwa. Ta bukaci a rika ba ilimin mata muhimmanci kasancewar rayuwa sai […]
Farfesa Amina Abubakar Bashir ta shafe shekara 30 tana koyar da Turanci a Jami’ar Maiduguri, ta rike mukamai da yawa a jami’ar. Ta yi bayanin yadda ta yi gwagwarmayar neman ilimi da kuma koyarwa, da yadda ta hada lura da iyali da kuma koyarwa. Ta bukaci a rika ba ilimin mata muhimmanci kasancewar rayuwa sai da ilimi take tafiya daidai.
Tarihin Rayuwata
Assalamu alaikum, sunana Farfesa Amina Abubakar Bashir. An haife ni shekarar 1960 a Gundumar Fika da ke karamar Hukumar Potiskum, a yanzu Jihar Yobe ke nan. Mahaifina ya yi karatun hada magunguna, kuma jigo a kungiyar masu hada magunguna ta Arewacin Najeriya. Bayan ya yi ritaya ne sai ya bude masana’antar hada magunguna mai suna Daya Pharmacy. Daga nan aka nada shi Galadiman Potiskum. Kuma shi ne Hakimin Goya.
Na fara firamare a Central Primary School da ke Nguru, Jihar Yobe, da yake mahaifina ma’aikacin gwamnati ne don haka bayan an yi masa canjin wurin aiki zuwa Maiduguri sai aka sanya ni a St. Patricks’ Primary School, amma na kammala firamarena a St. Theresa Primary School bayan an sake yi wa mahaifina canjin wurin aiki. Na kammala Kwalejin Gwamnatin ’Yan Mata da ke Maiduguri a shekarar 1977. Daga nan na fara karatu a College of Arts and Science da ke Mubi, Jihar Adamawa, bayan lokaci kadan sai na samu shiga Makarantar Share Fagen Shiga Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, bayan mun yi jarrabawa sai aka ba ni kwas din Turanci a jami’ar, inda na kammala digirina a shekarar 1981. Na yi digiri na biyu a Jami’ar Maiduguri, sannan na yi digiri na uku a Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya.
Na fara koyarwa a Jami’ar Maiduguri tun a shekarar 1981, bayan na yi shekara 20 a jami’ar sai na fara tunanin ya kamata in fara wani sabo, amma sai na ce bari in shekara 30 a jami’ar, cikin ikon Allah kuma sai ga shi Gwamnatin Tarayya ta bullo da jami’o’inta, wanda ya sanya na canja wurin aiki.
Abubuwan da ba zan manta da su ina karama ba
Na taso a gidan yawa ne, a lokacin komai na tafiya daidai kuma cikin sauki. Kusan kowane karshen mako mahaifina yakan dauke mu daga Nguru zuwa Potiskum. Mukan tsaya a wurare da yawa, muna da tafiya da abincinmu ne. Muna cikin tafiya za mu tsaya, sai kowa ya fito a shimfida taburma, mu ci; mu sha, sannan a yi hira. Wani lokaci mukan shiga daji don mu tsinki ’ya’yan itatuwa, mun yi rayuwar jin dadi a lokacin.
Haka lokacin da muke Yola, Jihar Adamawa, mukan je karamar Hukumar Numan inda muke shiga jirgin ruwa ana yawo da mu. Yanzu ba karamin takaici nake ji ba kasancewar ba mu yi wa ’ya’yanmu haka ba.
Burina ina karama
A lokacin da nake makarantar sakandare na karanta bangaren science ne, amma bayan na kammala musamman ma lokacin da na shiga makarantar share fagen shiga jami’a, mun shiga makarantar ne kafin sakamakon jarrabawar WAEC ya fito, a lokacin da sakamako ya fito sai na shiga tashin hankali domin pass nake da shi a darasin Chemistry, har na yanke shawarar barin makarantar sai na kai kukana wurin shugaban makarantar a lokacin Farfesa Angulu, na fada masa na yanke shawarar barin makarantar saboda ban san abin da zan yi ba, daga nan ya ba ni shawarar yadda zan yi, wanda hakan ne ya sanya na koma bangaren social science, don haka sai burina na zama injiniyar zane-zane gidaje (Architect) ya canza.
Shakuwa tsakanin iyaye
Na fi shakuwa da mahaifina, kasancewar tamu ta zo daya, musamman ma da yake na dauki bangaren ilimi, shi ma kuwa ya fi mayar da hankali kan ilimi ne. A yanzu mahaifinmu ya canza, amma a da ba ya aurar da ’yarsa ba tare da tana ajin karshe na jami’a ko ta kammala jami’a ba. ’Ya’yan mahaifinmu daga na farko zuwa na karshe duk sun yi digiri.
Farin cikin zama uwa
Na fara aiki ne ina da shekara 21 a Jami’ar Maiduguri. A lokacin ina da aure amma ban haihu ba, don haka ban sha wahala ba, na fara yaba wa aya zakinta ne wajen hada aiki da kuma lura da gida ne, bayan na fara haihuwa. Ni dai ban san ta yaya na iya tafiyar da aikin gida da kuma koyarwa ba, Allah ne Ya taimake ni har ga shi yanzu duk ’ya’yana sun yi jami’a, sun girma, suna kuma aiki.
Nasarori
Na samu nasarori da dama, musamman ma idan na duba yadda abubuwa suka rika tafiya mini daidai. Idan na kalli ’ya’yana da kuma matsayin da nake kai sai in rika gode wa Allah (SWT), mun yi aiki tukuru kuma Allah Ya taimake mu.
Karatun mata
Wannan shi ne abin da har yanzu muke fama da shi, idan muka kalli halin da ake ciki yanzu mun san akwai gibi sosai a bangaren ilimin mata. Haka idan muka koma bangaren iyali za mu ga ba a ba ilimin mata muhimmanci, idan har na ce zan yi magana a kan dalilin da ya sa ba a ba mata damar yin karatu sai mu kai gobe ba mu kammala tattaunawa ba. karamar hukuma da jihohin arewa duk ba su ba ilimin mata muhimmanci ba. Don haka ya kamata a mayar da hankali sosai ga bangaren ilimin mata. Kodayake an fara yin haka din, amma dai ana bukatar a sake zage damtse kan ilimin mata. Akwai abubuwa da dama, amma abin da nake so a fahimta shi ne, ya zama dole mu dauki batun ilimin mata da muhimmanci.
Abin koyi
Nakan yi koyi da duk wani da na ga ya mayar da hankali kan harkokin ci gaba da ya sanya a gabansa. kwazo da aiki tukuru nake fara dabuwa ga duk wanda zan yi mu’amala da shi. Idan kana da wani buri, sannan sai ka dage wajen cim ma burin, idan na lura da haka sai ka zama abin koyi a wurina.
Yadda nake hada aikin gida da koyarwa
A yanzu komai na tafiya cikin sauki saboda ’ya’yana duk sun manyanta, dan autana yana digiri na biyu, don haka ina samun isasshen lokaci wajen bangaren koyarwa, amma na sha wahala a lokacin da na fara haihuwa. Farin ciki a rayuwa
Farin cikina a rayuwa shi ne, yadda nake koyar da mutane har su zama cikakkun mutane. Ina alfahari da koyarwar da nake yi, domin ba kowa ne zai iya kai matsayin da na kai a harkar koyawar ba. Muna da dimbin mutane da suke ikrarin su malamai ne, amma a zahirin gaskiya su ba malamai ba ne. Babban farin cikin da nake yi shi ne da yawa daga cikin wadanda suka shiga jami’a ba su san ciwon kansu, amma ta hanyar yadda muke koya musu sai ka ga sun zama cikakkun mutane.
Yadda nake hutawa
A lokacin da nake hutawa nakan karanta littattafan labaran kirkira, wani lokaci nakan karanta mujallu ko na kalli talabijin ko kuma in shakata a lambuna. Wata hanya da nake hutawa kuma ita ce, in rika hira da abokai ko kuma in rika tafiye-tafiye. Na ziyarci wuraren shakatawa masu yawa a lokacin da na samu hutu, don haka duk wurin da na samu kaina nakan tabbata na samu cikakken hutu.
Yadda na hadu da mijina
Na hadu da mijina tun ina Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, wasa-wasa muka fara soyayya, sai ga shi mun yi aure mun hayayyafa, ya kuma taimaka mini na cim ma burina ta bangarori da dama.
Tufafi
Ban cika son kayan kyale-kyale ba, na fi son in sanya tufafin da za su rufe jikina, wadanda ba za su takura mini ba, ko su sanya in rika tsarguwar da ke nuna na sanya tufafin da ba su dace ba. Nakan sanya tufafi iri daya, misali, in sanya riga da zane da gyale da takalma da kuma agogo iri daya.
Abin da nake a tunani da shi
Ina so yara mata su dauke ni a matsayin wacce ke ba su kwarin gwiwa. Ina so in zama mace abar koyi a duk inda na zauna. Ba na so a rika alla-wadai da ni, ko a rika fadar wadansu munanan halaye game da ni. Ina so kuma a dauke ni a matsayin wacce ta ilimantar da al’umma.
Shawara ga mata
Ina kira ga mata da su mike tsaye su nemi ilimi, su fahimci babu rayuwar da za ta tafi daidai ba tare da ilimi ne sitirayinta ba. Duk wanda yake yin abu a cikin duhu sai ya jefa kansa ga halaka ba tare da ya sani ba.