Farfesa Comfort Nanko: Akwai kalubale a aikin koyarwa

Farfesa Comfort Nanko Piwuna ita ce Kwamishiniyar Kimiyya da kere-kere ta Jihar Filato. Ta yi bayanin kalubale da kuma nasarorin da ta samu wurin aikin koyarwar a jami’a.  Haka kuma ta bayyana mahimmancin neman ilimi ga ’ya’ya mata.TarihinaSunana Farfesa Comfort Nanko Piwuna. A yanzu ina da shekara 50. An haife ni a karamar Hukumar Langtang […]

Farfesa Comfort Nanko: Akwai kalubale a aikin koyarwa
Farfesa Comfort Nanko: Akwai kalubale a aikin koyarwa

Farfesa Comfort NankoFarfesa Comfort Nanko Piwuna ita ce Kwamishiniyar Kimiyya da kere-kere ta Jihar Filato. Ta yi bayanin kalubale da kuma nasarorin da ta samu wurin aikin koyarwar a jami’a.  Haka kuma ta bayyana mahimmancin neman ilimi ga ’ya’ya mata.
Tarihina
Sunana Farfesa Comfort Nanko Piwuna. A yanzu ina da shekara 50. An haife ni a karamar Hukumar Langtang ta Arewa, a Jihar Filato, amma na girma a garin Jos. Na yi makarantar firamare a Township  Primary School da ke Jos. Na yi makarantar sakandare a Jihar Nasarawa.  Daga sai makarantar S.B.S.  Keffi a Jihar Nasarawa. Bayan haka na yi aiki a wani asibiti mai suna New Crescent da ke Jos na tsawon shekara 2. Daga nan na tafi Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, inda na yi digirina na farko kan Nazari kan hallitu masu rai. Bayan na kammala digiri ne sai na yi hidimar kasa a Legas, inda na koyar a makarantar sakandare ta sojojin sama da ke Ikeja.
Na yi digiri na biyu kan halittu masu rai a Jami’ar Jos. Daga nan na fara koyarwa a Makarantar Horon Malamai da ke kan hanyar Zariya. Na yi kamar shekara 3 ina wannan aikin koyarwa. Daga nan Jami’ar Jos ta dauke ni aikin koyarwa tun a shekarar 1992. Har ya zuwa wannan  lokaci da mai girma Gwamnan Jihar Filato Jonah Jang ya nada ni a matsayin Kwamishinar Ma’aikatar Kimiyya da kere-kere ta Jihar Filato.
Nasarori
Akwai nasarori da dama da zance na samu. Ka ga kamar a bangaren koyarwa, babbar nasarar da zan ce na samu  ita ce, akwai yara da dama da na koyar wadanda a yanzu sun samu manyan mukamai, kuma suna yi mini waya, suna yi mini godiya kan yadda na rike su, na kuma koyar da su.  A lokacin da nake koyarwa akwai yara da dama da suke zuwa suna kawo mini kuka kan cewa iyayensu ba su da kudin da za su biya musu kudin makaranta, a lokacin nakan taimaka musu da abin da nake da shi. Akwai masu zuwa da damuwar rashin lafiya ko ta gidajensu, duk nakan yi iyakar kokarina wajen taimaka musu. Yanzu irin wadannan yara akwai wadanda suka zama daktoci, akwai wadanda suka zama malamai da wadanda suka zama manya a fannonin rayuwa daban-daban. A gaskiya a kullum idan na tuna irin  wadannan nasarori da na samu ta fannin aikin koyarwa, nakan yi matukar  farin ciki.
A bangaren ma’aikatar kere-kere da aka nada ni kwamishina kuma, na samu nasarori da dama. Ko a kwanakin nan mun shirya wa kwamishinoni da shugabannin hukumomin gwamnatin jiha da manyan sakatatorin hukumomin gwamnati da masu ba gwamna shawara na musamman taron bita kan ilmin kwamfyuta.
Haka kuma za mu shirya wa dukkan ‘yan majalisar dokokin jihar nan da dukkan ma’aikatan jihar nan irin wannan taron bita kan ilmin kwamfyuta. Kuma muna nan muna shirin ganin mun koya wa dukkan mutanen Jihar Filato ilmin kwanfyuta. Mun fito da wannan shiri ne ganin cewa an bar Jihar Filato a baya kan ilmin kwamfyuta. Kuma  a wannan zamani da muke ciki komai za ka yi sai da kwamfyuta.  A wurina wannan wata babbar nasara ce.
Bayan haka a yanzu haka wannan ma’aikata tana da wata gona a karamar Hukumar Langtang ta Kudu. A shekara 2 da suka gabata, mun samu wani irin rogo na musamman daga Ibadan,  wanda yake girma da wuri, mun je mun shuka shi a wannan gona. Bayan da ya yi mun cire shi mun yanyanka shi, mun raba wa manoman yankin, a yanzu manoman yankin suna amfani da wannan rogo.
Bayan haka akwai wata cibiyar sarrafa kayayyakin kimiyya da kere-kere da ke karkashin wannan ma’aikata  a Laranto da ke nan cikin garin Jos. Kafin na zo, wannan cibiya ta riga ta mutu, babu wani aiki da ake yi a wajen, duk injinan da ke wajen sun yi tsatsa. Amma bayan na zama kwamishina sai muka nemi kudi daga wajen gwamna, muka sake farfado da wannan waje. A yanzu muna sarrafa kayayyakin kimiyya da kere-kere  da za a rika raba wa makarantun sakandare da ke wannan jiha.
Akwai wata cibiyar kera injina da karafun  mota da yin man shafawa da man gashi da gwamnatin tarayya ta kafa  a garin Bukur, a yanzu mun hada hannu da Gwamnatin Tarayya wajen kafa wannan cibiya, muka ba su fili, muka yi musu gina, muka yi musu  hanyar mota da sanya musu ruwa da wutar lantarki.   Wannan ma wata babbar nasara ce a gare ni.
Na tura ma’aikatan wannan ma’aikata da dama zuwa wurare daban-daban don su karo ilmi da kwarewa.
kalubale
Akwai kalubale da dama musamman yadda da ake ganin akwai abubuwa da dama da ba su kamata  mata su yi ba. Ba wai maza kwai Allah Ya ba wa kwakwalwa ba, Allah Ya bai wa maza da mata. To, a takaice kalubale na farko ke nan da na fara fuskanta. Ni duk rayuwata a aikin koyarwa na yi ta, kamar yadda na fada. Akwai daliban da za ka ga idan sun ga kamar ke mace ce za su iya miki rashin hankali, su yi miki maganar da ba ta kamata ba. Wannan yana daga cikin kalubalen da na fuskanta. Amma da na rike mutuncina sai irin wadannan dalibai suka ga cewa irin wannan rashin hankali ba zai kai su ko’ina ba.
Bayan haka akwai kalubale kan yadda mutum zai tafiyar da iyali. Ina jami’a na yi aure. Don haka lura da iyali ga makaranta akwai ‘yar damuwa. Amma na kasa lokacin aiki da lokacin kula da iyali. Bayan haka a lokacin da aka nada ni kwamishina sai na zama bakuwa, domin kamar yadda na fada ni rayuwata gaba daya a aikin koyarwa na yi. Don haka sai da na zauna na koyi wannan sabuwar rayuwa tukunna kan yadda zan yi hulda da jama’a. Ka san mai aikin koyarwa babu wani ciwon kai da zai fuskanta. Amma a lokacin da na zama kwamishina ban samu abin da sauki ba, na fuskanci kalubale sosai, domin tafiya da jama’a musamman ‘yan siyasa sai da hakuri.
kungiyoyi
Ina cikin kungiyoyi da suka hada da kungiyar Malaman Kimiyya Mata  na Jami’a, kuma ina cikin kungiyar Malamai Mata Masu Koyarwa a Jami’a kuma ina cikin kungiyar mata masu aikin yada bishara a coci-coci.
Siyasa.
A gaskiya ba ni da ra’ayin siyasa. Burina bayan na kammala wa’adin wannan kujera ta kwamishina in koma aikina na koyarwa.
Abin da nake sha’awa a lokacin da nake karama
A lokacin da nake karama na yi sha’awar in zama mai aikin hada magungunan (Phamacy). Don a takardar neman shiga jami’a da na rubuta ma abin da na nemi su ba ni in karanta ke nan.
Iyali
Ina da miji da ’ya’ya uku; namiji daya da mata biyu. A halin yanzu namijin yana digirinsa na biyu, daya macen ta gama digiri, dayar kuma a halin yanzu tana digiri.
kasashen da na ziyarta
Na ziyarci kasashe da dama kamar Dubai da Kanada da Ingila da Afirka ta Kudu da Jamhuriyar Binin da dai sauransu.
Mata a harkar ilimi
A gaskiya ina gode wa mata da iyayensu kan yadda suka rungumi neman ilimi, domin babu shakka a halin yanzu mata sun ci gaba kan wajen neman ilmi. A da iyaye ba sa barin mata su yi karatu, sai a yi wa mata aure tun suna kanana. Amma a yanzu idanun mutane sun bude, sun gane cewa, akwai amfanin mata su tafi makaranta. Idan mace ta yi karatu akwai amfani da dama, domin iyayenta za su amfana, iyalinta za su amfana, al’umma za su amfana gaba daya, saboda haka ina kira ga iyaye su ci gaba da barin ‘ya’ya mata su rika karatu.
Burina bayan ritaya
Burina bayan na yi ritaya shi ne, in rungumi noma musamman kiwon  kifi da kiwon kaji.
Tufafi da Abinci
Na fi son tufafinmu  na gargajiya. A bangaren abinci na fi son tuwon shinkafa da miyar yakuwa.
Shawara ga mata
Shawara ta ga mata ita ce, su tashi tsaye su taimaki kansu, domin idan ba su tashi sun taimaki kansu ba, babu wanda zai tashi ya taimake su. Mu mata Allah Ya ba mu murya. Ni ban ce mata su yi fada da mazajensu ba, amma mata su lallabi mazajensu don a tura ‘ya’ya mata makaranta. Kuma iyaye mata su nemi abin yi, domin yanzu komai na rayuwa akwai wahala. Idan mata suka bar wa maza komai za su iya kasawa. Don haka dole ne mace ta tashi ta nemi wani abin yin da zai kawo mata kudin da za ta iya taimaka wa maigidanta, ko ta wajen biya wa yara kudin makaranta ko sayen magani ko gyaran gida.