Farfesa Dora Akunyili ta rasu
Tsohuwa Ministar Watsa Labarai, Farfesa Dora Nkem Akunyili ta rasu a wani asibitin kasar Indiya sakamakon fama da ciwon sankara.Farfesa Dora Akunyili wadda ta taba zama Darakta Janar tta Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta kasa (NAFDAC) fitacciyar masaniyyar harhada magunguna ce, kuma malamar jami’a kuma kwararriya a fannin gudanarwa.Ta ajiye mukaminta na […]

Tsohuwa Ministar Watsa Labarai, Farfesa Dora Nkem Akunyili ta rasu a wani asibitin kasar Indiya sakamakon fama da ciwon sankara.
Farfesa Dora Akunyili wadda ta taba zama Darakta Janar tta Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta kasa (NAFDAC) fitacciyar masaniyyar harhada magunguna ce, kuma malamar jami’a kuma kwararriya a fannin gudanarwa.
Ta ajiye mukaminta na Ministan Watsa Labarai a ranar 16 ga Disamban 2010 domin ta tsaya takarar Sanata daga mazabar Anambra ta Tsakiya.
Lokacin da take Hukumar NAFDAC ta samu lambobin yabo a ciki da wajen Najeriya sakamakon yadda ta tsaya kai da fata wajen yaki da miyagun kwayoyi.
An haifi marigayiyar a Makurdi ta Jihar Benuwai a ranar 14 ga Yuli, 1954, kuma ita ’yar asalin kauyen Nanka ne da ke Jihar Anambra.
Ta fara karatu a makarantar St Patrick’e Primary School da ke Isoufia a Jihar Anambra inda ta kammala a 1966, sai ta samu takardar shaida ta Afirka ta Yamma (WASC) da daraja ta kololuwa a 1973 daga makarantar sakandare ta kueen of the Rosary Secondary School da ke Nsukka.
Kuma sakamakon kwazonta a jarrabawar ne Gwamnatin Jihar Gabas da Gwamnatin Tarayya suka ba ta tallafin karo ilimi, inda ta yi digirinta na farko a harhada magunguna a 1978 da kuma digiri na uku a Jami’ar Nsukka.
Wakiliya ce a cibiyoyin kwarewa da dama a Landan da Najeriya da Afirka ta Yamma. Kuma ana sa ran isowar gawarta kasar nan zuwa karshen wannan mako.