Farfesa Ghaji Badawi: Aure ba ya hana ilmi
Farfesa Ghaji Abubakar Badawi malama ce a Sashen Library and Information Science a Jami’ar Bayero Kano. A gidan mijinta ta yi karatu har ta kai ga matsayin Farfesa kuma ta dauki tsawon shekaru 10 tana gudanar da bincikenta na Farfesa a barikin karuwai na Gadar Tambaruwa. Tarihin Rayuwa Sunana Ghaji Abubakar Jakada amma bayan na […]
Farfesa Ghaji Abubakar Badawi malama ce a Sashen Library and Information Science a Jami’ar Bayero Kano. A gidan mijinta ta yi karatu har ta kai ga matsayin Farfesa kuma ta dauki tsawon shekaru 10 tana gudanar da bincikenta na Farfesa a barikin karuwai na Gadar Tambaruwa.
Tarihin Rayuwa
Sunana Ghaji Abubakar Jakada amma bayan na yi aure sai sunana ya canza zuwa Ghaji Abubakar Badawi. An haife ni a garin Wudil cikin Jihar Kano lokacin mahaifina yana aikin alkalanci a can. Sai dai daga baya mun dawo gidanmu na Kano a unguwar Magashi. Mahaifina ya kasance mutum ne mai son ilimi musamamn ma ilimin ‘ya’ya mata. ‘Yarsa ta fari ba ta yi karatun boko ba, saboda al’adar bahaushe mutum ba shi da iko da dan fari. Don haka ya dora burinsa na karatu akanmu ni da wata yayar tawa. A lokacin saboda doki tun ina shekara biyar aka sanya ni a Makarantar firamare ta Shekara. Sai dai da yake Allah Ya kadarta ba za mu yi karatu mai tsawo a wanann lokacin ba, sai mahaifinmu ya tafi Alkahira yin karatu. Hakan ya sa muna aji bakwai yayan mahaifinmu wanda dama ba ya son karatun mata ya yi mana aure. Ni ban san ma mijin ba sai a lokacin da aka yi auren. Ina gidan miji na samu ciki a lokacin shekararta 14, to saboda kankantata sai likita ya bayar da shawarar a yi min tiyata. A nan aka cire min dana na fari. Yaro ya samu watanni da haihuwa mahaifina ya dawo daga Alkahira, inda ya tausaya wa halin da nake ciki. Ganin irin wahalar da na sha a haihuwa ya sa ya bai wa mijina zavi ko ya mayar da ni makaranta ko kuma a kashe auren. Sai maigidan nawa ya ki yarda da batun komawata makaranta. karshe dai aka kashe aurena na koma makaranta. A nan ne na shiga makarantar sakandaren al’umma ta Kano wacce aka fi sani da KCC. Ba na mantawa ajinmu daya da tsohon Gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekarau. Sai dai a wanann makaranta na hadu da maigidana na yanzu lokacin ina aji biyu sai muka yi aure. Muna nan tare ina kuma karatuna har na haifi yara biyu. Sai ya samu tallafin karatu ya tafi kasar Ingila. Da yake tare muka tafi sai ya sa na koma makaranta a can har na rubuta jarrabawata ta GCE. Bayan mun yi shekaru kamar biyar a can sai muka dawo gida inda bayan na haifi ‘yar autata A’isha. Sai maigidana tare da yayana Gambo Jakada suka shawarce ni da na koma makaranta na yi diploma a BUK. A lokacin shekarata 26 da haihuwa sai na ga ai na yi tsufa da karatu. Da kyar dai suka shawo kaina na yarda na koma To bayan na kammala a shekarar 1989 sai na fita da sakamako mafi kyau distinction a sashen Library Science. Ganin kyakkyawan sakamakona sai shugaban sashen ya nemi da na zarce na yi digiri. A lokacin ba a wa mutum digiri kai tsaye sai ya je ya yi aiki na tsawon shekara guda. Haka dai da karfin gwiwar maigidana da na dan uwana na koma karatu a karo na biyu. Sai dai muna shekarar karshe sai shugaban sashen namu ya kira ni ya gaya min cewa suna ganin zan fita da sakamako mai kyau don haka za su ba ni aikin koyarwa a sashen nasu. Da na je na gaya wa maigidana sai ya yarda. Da na kammala digirina a shekarar 1992 sai suka ba ni aiki. Bayan na fara aiki sai na koma na ci gaba da karatun digiri na biyu. Bayan na kammala nan ma shuganbannin da maigidana suka ci gaba da karfafa min gwiwa na yi digiri na uku. Daga nan na ci gaba da gudanar da bincike da gabatar da makaloli daban-daban. Sannan na gudnar da bincikena na zama farfesa akan karuwan Gadar Tamburawa a Jihar Kano, binciken da ya dauke ni tsawon shekaru 10 kafin na kammala. Daga nan ne kuma bayan na gabatar da laccata a cikin shekarar nan aka ba ni mukamin cikakkiyar farfesa.
Iyali:
A yanzu ina tare da maigidana Alhaji Abubakar Badawi. Mun haifi ‘ya’ya uku tare da shi, maza biyu sai ‘yar autata mace. Musbahu ne babban dana da na haifa a aurena na farko. A yanzu haka yana gudanar da aikinsa na kansa. Sai Abdullahi da yake aiki a Ma’aikatar kananan hukumomi Sai Ahmad da yake aiki a First Bank. Sai ‘yar auta A’isha wacce ke da ‘ya’ya biyu. Haka kuma a yanzu tana can tana karatun digirinta na uku a Dhabi. Duk abin da na zama a rayuwata maigidana ne sila. Maigidana irin mutanen ne da suka damu da iyalinsu. Ina iya tunawa lokacin da nake karatu ko takarda na saya ta Naira 20 to sai ya ba ni kudina. Ya taimaka min kwarai da gaske sai dai Allah Ya biya shi. Idan mace ba ta da taimakon mijinta dari bisa dari a harkar karatunta to ba za ta ci nasara ba.
Ya kike ganin hazakar dalibai a wannan lokaci?
Ba za a tava kwatantawa ba domin ni a yanzu ina mamakin yadda dalibai suke. dalibai ba sa karatu, masu wayo ne ma ke karatu sosai a lokacin jarrabawa. Wasu kuwa sun dogara da satar ansa. Ina mamakin yadda dalibi zai rubuta wa malami amsar abin da ya ba shi wannan ya nuna ba ya yin karatu ballantana bincike. dalibai ba sa mayar da hankali ko kadan. Da zarar ka duba takardun jarrabawarsu za ka ji kamar ka yi ihu saboda vacin rai, ka rasa ta yadda za ka taimakawa dalibi saboda bai san komai ba ballantana ka dan taimaka masa ya haye sai dai a yi ta zagin malamai. A kulluma nakan yi kokari na kwatanta hazakar daliban da da na yanzu sai na ga ba mahadi ko kadan. Ni da ma mutum ce mai son karatu, haka kuma ba na son na zama ta biyu. Na fi so a kullum a ce ni ce a gaba. Ina iya tuna lokacin da nake karatu duk da cewa akwai nauyin iyali a kaina amma in har ba ni da lacca to ina dakin karatu. Ba na mance wa da wani abu da ya faru wata rana ina cikin dakin karatu ina karatu har karfe 10:30 na dare ashe ban sani ba har an rufe dakin karatun ina ciki. Sai da mai kula da wurin ya zo ya gan ni ina ta karatuna yake gaya min cewa ai shi har ya rufe dakin karatun sai daga baya ya gano bai kashe fitilar sashen da nake ba, shi ya sa ya dawo ya kashe. Idan dalibi yana son samun abinda yake so to dole ya auri dakin karatu. Haka kuma idan mutum yana yin abu to ya kamata ya yi shi da gaskiya. A kulluma kokari nake na ga na ga ina samun ci gaba a harkar gudanar da aikina, don haka a duk inda na ji labarin za a yi taro na vangaren karatuna to nakan halarta a ko’ina ne cikin duniyar nan. Wannan dalili ya sa na samu damar ziyarar kasashe daban daban a duniya tun daga Amurka da Koriya da China da Norway da Dhabi da Ajantina da Moscow da Nepal da Masar da South Africa da Durban da Kenya da Senegal da sauransu. Nakan yi amfani da kudin albashina na je na hadu da jama’a da suka yi fice a vangaren karatuna. A irin wannan haduwa ne nake samun karin ilimi nake kuma sanin sabbin abubuwa a vangren da nake koyarwa da sauransu.
Nasarorin da na samu:
Ni dama ina da naci, duk abin da na sa gaba ina yin sa mai kyau. Ban yarda na sa kaina yin abu, sannan na yi shi da wasa ba. Babu shakka na samu nasara a harkar karatuna da aikina. A kulluma malamaina sukan buga misali da ni
kalubale:
Ba za a rasa kalubale nan da can ba a rayuwa. Na samu matsaloli a wurin aiki amma ba yawa. babban abin da yake damuna a yanzu shi ne yadda zumunci ya lalace. Sai ka ga ‘yan uwa, uwa daya uba daya amma ko magana ba sa yi da juna. Wannan abu yana yi min ciwo kwarai da gaske. Ban san abin da malaman addini za su iya yi a wannan vangare ba.
Buri:
Ina ganin burina ya cika, wato na son koyarwa. A wurin koyarwa nake samun farin ciki, a duk inda nake ba na samun farin ciki sai a gaban dalibai. Ba na jin ni wata ce sai ina gaban dalibai. Nakan iya barin duk abin da nake yi na je na koyar da dalibai. Ina ganin koyarwa a cikin jinin gidanmu take, mahaifina malami ne. haka kuma tun daga kaina har zuwa kan ‘yar autar gidanmu malaman makaranta ne.
Abin da take son bari a bayanta:
Ina so na ga wata rana a wayi gari garin Gadar Tamburwa wanda ya yi suna a wani tsibiri na karuwanci ya canza fasali zuwa wani babban gari na ilimi da ci gaba. Ya zama gari na nunawa na kwatance. Daga yadda take a shekarun baya tun 1954 ta canza ta zama gari na nunawa. Zuwa yanzu dai na aike wa ma’aikatun lafiya da na mata na Jihar Kano takardu akan irin tunanin da nake da shi ma’ana hanyoyin da za bi a bunkasa jin dadi da walwalar jama’ar garin. Haka kuma zan yi amfani da wannan dama wajen yin kira ga masu hannu da shuni da su tallafa wa wannan gari. Kasancewar a binciken da na yi na tsawon shekaru 10 a wanann gari na gano cewa ba wai dadi ne yake zaune da mutane a wanann wuri ba illa bakin ciki na yunwa da ciwo da talauci. Yawanci ma na gano cewa talauci shi ne ulmulaba’hisin shigar mafi yawansu karuwanci. Babu matar da take shiga karuwanci don son ranta sai dole. Sai kin shiga cikinsu za ki tausaya wa rayuwarsu. Karuwa za ta haihu saurayin ya gudu ya bar ta. Ada ina tunanin zan iske rayuwarsu mai inganci amma lokacin da na fara zuwa sai na ga abin ba haka yake ba. Matan nan suna bukatar taimako, amma muna kallonsu ba za mu taimaka musu ba sai dai mu zage su, sannan muna kiran kanmu Musulmi? Ina da yakinin cewa idan aka yi haka karuwanci zai zama tarihi a wannan wuri, domin a halin yanzu ma tuni da yawa daga cikinsu sun bar karuwanci. Akwai wani babban gidan giya a garin ana kiran sa gidan Anthony yanzu ya zama dakin shan magani, ma’aikatar lafiya ta Jihar Kano ce ta yi wannan aiki. Ba na mancewa wata rana da na je garin na tarar wata karuwa ta mutu, ga gawa na shimfide ba akai ga binne ta ba, amma kafin ki ce kwabo an sace komai na dakinta. Wanann abu ya ba ni tsoro matuka. Da na dawo gida sai na fara tunani me ya sa yaran mata za su sanya kansu cikin wanann rayuwa. A karshe na gano talauci ne ya jefa su a cikin wannan mummunan rayuwa. Yawanci iyayensu ba su da karfin daukar nauyinsu. Iyayen da yawa