Farfesa Ghaji Badawi: Aure ba ya hana ilmi (2)

daga cikinsu murna suke da tafiyarsu domin a ganinsu baki ya ragu. Mun bayar da shawara ma’iaktar ilimi ta bude musu makaranatar yaki da jahilci, domin a tattauna da su sun nuna suna son karatu, sai dai sun hakura ne saboda ba su da yadda za su dauki nauyin kansu. Daga binciken da na gabatar […]

Farfesa Ghaji Badawi: Aure ba ya hana ilmi (2)
Farfesa Ghaji Badawi: Aure ba ya hana ilmi (2)

daga cikinsu murna suke da tafiyarsu domin a ganinsu baki ya ragu. Mun bayar da shawara ma’iaktar ilimi ta bude musu makaranatar yaki da jahilci, domin a tattauna da su sun nuna suna son karatu, sai dai sun hakura ne saboda ba su da yadda za su dauki nauyin kansu. Daga

binciken da na gabatar mata kadan ne suke shiga karuwanci don dalilin auren dole. To akwai ma karuwan da ba a taba yi musu aure ba a cikinsu yara kanana.
Abin koyi a rayuwarta:
Mahaifina shi ne abin koyi a wurina. Idan akwai na biyu sai maigidana Abubakar Badawi. Idan aakwai na uku kuma shi ne dan uwana Gambo Jakada.
Shawara ga mata:
Shawarata ga mata ita ce su dage su nemi na kansu, ko dai ki yi karatu ko kuma ki yi sana’a. Zama ba zai yiwu haka ba. A duk lokacin da ya zama kina da abin yi to kin fi karfin wulakancin namji. Domin ko da ya yi niyyar yada ke, to da kafafuwanki za ki dire. Kullum abin da nake gaya wa mata shi ne su dage su nemi abin kansu. Ki tsaya ki lallabi mijinki ya bar ki, ki yi karatu ko ki yi sana’a. Ilimin mace na addini da na boko yana da muhimmanci wajen tarbiyyar ‘ya’yanta. Haka kuma akwai bukatar mu zama jagora ga ‘ya’yanmu cikin duk abin da suke yi a rayuwa, kada mu sake su sasakai. Ko da a bangaren zabin karatu mu taya su zabar bangaren da za su karanta, idan kika ga zai bi hanyar da ba za ta bulle da shi ba, to ki kira shi ki nuna masa hanya mafi dacewa da shi. Akwai bukatar mata mu rika kula da kanmu ta fuskar lafiyarmu. Cututtuka sun yi wa mata yawa. mu rika taimaka wa kanmu da motsa jiki. Za ki samu wata matar sai ta yini a gaban akwatin talabijin ba tare da ta tashi ba, sai dai masu aiki su yi mata komai. Ni fa har yanzu ni nake ayyukan gidana da kaina. Mata su kula da abincin da suke ci masu lafiya. ba wai mai tsada ba, a’a masu gina jiki irinsu ganyayyaki da kayan itatuwa. Zan yi amfani da wannan dama na yi kira ga maza da su tallafa wa matansu la’alla ta hanyar karatu ne ko ta sana’a domin lokaci na zuwa da za su ga amfanin hakan ga rayuwarsu da ta ‘ya’yansu kai har da ta jikokinsu. A lokacin da karfinka ya kare ita kuma sai ta tallafa wa iyalinku da dan abin da take samu.