Farfesa Jega ya koma koyarwa
Shugaban Hukumar Zabe ta kasa (INEC) da ya sauka a makon jiya Farfesa Attahiru Jega ya koma aiki a Jami’ar Bayero da ke Kano, inda yake koyarwa kafin tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya nada shi shugabancin Hukumar INEC a shekarar 2010. Farfesa Jega wanda ya bar jami’ar shekara biyar da suka gabata zuwa INEC […]
Shugaban Hukumar Zabe ta kasa (INEC) da ya sauka a makon jiya Farfesa Attahiru Jega ya koma aiki a Jami’ar Bayero da ke Kano, inda yake koyarwa kafin tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya nada shi shugabancin Hukumar INEC a shekarar 2010.
Farfesa Jega wanda ya bar jami’ar shekara biyar da suka gabata zuwa INEC ya kammala wa’adin shugabancinsa ne a ranar Talatar makon jiya.
Wakilinmu ya ce kafin Farfesa Jega ya shiga ofishinsa a sashin Kimiyyar Siyasa sai da ya ziyarci ofishin Shugaban Jami’ar Farfesa Abubakar Adamu Rashid, inda Aminiya suka ’yar gana kafin ya zarce ofishinsa wanda mahukuntan jami’ar suka gyara da misalin karfe 11: na rana.
Lokacin da yake maraba da tsohon shugaban Hukumar INEC din Shugaban Jami’ar Farfesa Abubakar Rashid ya ce jami’ar tana murna da dawowar Jega wanda ya bayyana shi da babbn jakadan jami’ar.
Ya ce: “Jami’ar Bayero tana alfahari da kai Farfesa Attahiru Jega, hakika kai kyakkyawan jakada ne ga wannan babbar jami’a,” ya ce sunan jami’ar ya kara daukaka sakamakon kyakkyawan aikin da Farfesa Jega ya yi, kuma jami’ar ba za ta taba mantawa da Jega ba saboda gudanar da zabe mafi inganci da adalci a tarihin kasar nan.
A takaitaccen jawabinsa Farfesa Jega ya shaida wa shugaban jami’ar cewa tun daga ranar da ya tafi aiki a INEC ya tafi ne da zimmar ya dawo jami’ar bayan karewar wa’adin aikinsa.
Farfesa Jega ya ce koyarwa ne aikin da ya fi sha’awa kuma wannan ne ya sanya ya dawo aji bayan kwana bakwai da sauka daga aikinsa na babban mai shirya zabe.
Ya yi alkawarin yin bakin kokarinsa wajen koyarwa da bincike da kuma bauta wa jama’a, inda ya nuna godiya kan kyakkyawar marabar da mutanen jami’ar suka nuna masa.
Farfesa Jega shi ne tsohon shugaban jami’ar na biyar da har yanzu suke aiki da jami’ar.
Sauran tsofaffin shugabannin hudu sun hada da Farfesa dandatti Abdulkadir da Farfesa Ibrahim H. Umar da Farfesa Bello Bako dambatta da kuma Farfesa Sani Zaharaddeen wanda har wa yau shi ne babban limamin Kano.