Farfesa Jibril Aminu na nan a raye
Binciken Aminiya ya gano cewa tsohon dan Majalisar Dattawa Farfesa Jibril Aminu na nan a raye, sabanin ji-ta-ji-tar rasuwarsa da aka yada a wasu kafafen. A ranar Alhamis ne dai aka yi ta rade-rade rasuwar tsohon Jakadan Najeriya Najeriya a Kasar Amurka, Farfesa Jibril Aminu, mai kimanin shekara 81. Yaron da iyayensa suka daure a […]
Binciken Aminiya ya gano cewa tsohon dan Majalisar Dattawa Farfesa Jibril Aminu na nan a raye, sabanin ji-ta-ji-tar rasuwarsa da aka yada a wasu kafafen.
A ranar Alhamis ne dai aka yi ta rade-rade rasuwar tsohon Jakadan Najeriya Najeriya a Kasar Amurka, Farfesa Jibril Aminu, mai kimanin shekara 81.
- Yaron da iyayensa suka daure a cikin dabbobi ya samu lafiya
- Yaron da iyayensa suka daure a cikin dabbobi ya samu lafiya
Sai dai na hannun damansa kuma Shugaban Jami’ar Tarayya ta Kashere a Jihar Gombe, Farfesa Umaru A. Pate, ya ce Farfesa Jibril na nan da ransa.
Farfesa Pate ya ce, “Babu gaskiya a labarin rasuwarsa, Farfesa na nan a raye; na yi magana da shi; An yi ta kiram mu ana tambaya game da gaskiyar labarin rasuwarsa, amma ina tabbatar maka cewa yana nan da ransa a gidansa da ke Abuja.”
Farfesa Jibril wanda kwararren likita ne ya kasance zababben dan Majalisar Dattawa mai wakiltar mazabar Adamawa ta Tsakiya a shekarar 2003 zuwa 2011.