Farfesa Kaita ya gargadi daliban Jami’ar Tarayya da ke Dutsenma

Shugaban Jami’ar Tarayya da ke Dutsinma a Jihar Katsina, Farfesa Haruna Abdu Kaita ya hori daliban jami’ar su kauce wa shiga kungiyoyin asiri da harkokin da za su lalata karatunsu musamman ganin yadda jami’ar take da kyakkyawan yanayi na koyo da koyarwa.Wata sanarwa da kakakin jami’ar Malam Isyaku Yusif Karofi ya sanyawa hannu kuma ya  […]

Farfesa Kaita ya gargadi daliban Jami’ar Tarayya da ke Dutsenma
Farfesa Kaita ya gargadi daliban Jami’ar Tarayya da ke Dutsenma

Shugaban Jami’ar Tarayya da ke Dutsinma a Jihar Katsina, Farfesa Haruna Abdu Kaita ya hori daliban jami’ar su kauce wa shiga kungiyoyin asiri da harkokin da za su lalata karatunsu musamman ganin yadda jami’ar take da kyakkyawan yanayi na koyo da koyarwa.
Wata sanarwa da kakakin jami’ar Malam Isyaku Yusif Karofi ya sanyawa hannu kuma ya  bai wa Aminiya ta ce Farfesa Haruna Kaita ya yi wannan gargadi ne a lokacin da ya gana da daliban bayan ya kama aiki a matsayin sabon shugaban jami’ar, inda ya ce da yardar Allah, jami’ar za ta ci gaba da kasancewa abar misali a tsakanin jami’o’in kasar nan.
Shugaban ya kuma kai ziyarar ban girma ga Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari da Mai martaba Sarkin Katsina Alhaji Abdulmumini Kabir Usman da Mai martaba Sarkin Daura Alhaji Umar Farouk Umar da Hakimin Dutsinma da sauran shugabannin al’umma na yankin, inda ya sha alwashin zai yi bakin kokarinsa wajen ciyar da jami’ar gaba ta yadda za ta ci gaba da samar da dalibai masu nagarta.
A jawabin Gwamna Masari ya tabbatar wa Shugaban Jami’ar da cewa gwamnatin jihar za ta bai wa jami’ar duk goyon bayan da take bukata domin ganin ana cimma nasarar aiki.
Sarkin Katsina ya bukaci sabon shugaban jami’ar ya gyara duk wasu kura-kurai da ya tarar a jami’ar, tare da fatar jami’ar za ta bunkasa a zamaninsa.
Farfesa Haruna Kaita ya kuma gana da manya da kananan ma’aikatan jami’ar inda ya tabbatar musu da cewa zai yi bakin kokarinsa wajen ganin cewa ana bai wa ma’aikata cikakkiyar dama ta gudanar da aiki tare da duba duk wata matsala da ke damunsu domin warware ta cikin yardar Allah.
Sanarwar ta ce daga zuwan sabon shugaban jami’ar kasa da mako biyu, ya yi kokarin fara samar da ayyukan inganta rayuwa a jami’ar da suka hada da sanya wutar lantarki da hanyoyi da ruwan sha.