Farfesa Pate ya fara aiki a matsayin Shugaban Jami’ar Kashere

“Bincike shi ne bambanta jami’a daga makarantar sakandare”

Farfesa Pate ya fara aiki a matsayin Shugaban Jami’ar Kashere

Farfesa Umaru Pate

Sabon Shugaan Jami’ar Tarayya da ke Kashere (FUK) a Jihar Gombe, Farfesa Umar Pate ya fara aiki matsayin Shguabanta na uku, tare da kira ga ma’aikata su ba da hadin kai don ciyar da ita gaba.

A jawabinsa a yayin bikin mika masa ragamar jami’ar, Farfesa Pate ya ce daukaka martabar Jami’ar na bukatar hadin kai da gudunmuwar kowane bangare, don haka yin kiran ke da muhimmanci.

“Har yanzu jami’ar tasowa take yi, shi ya sa ake bukatar hada kai domin daukaka darajarta ta zama abar sha’awa,” inji shi.

Farfesa Pati ya kuma yi alkawarin dorawa a kan nasarorin da jami’ar ta samu a baya da kuma zurfafa bincike, wanda “shi ne abin da ke bambanta jami’a daga makarantar sakandare.”

Ya kuma ce zai dage wajen jawo hankalin gwamnati, da masu hali su taimaka wajen gina gidajen ma’aikata, samar da kudade da kuma karin gine-gine a jami’ar, don samar da yanayin da zai dace da ilmantarwa da bincike.

A watan Disamban 2020 ne aka nada Farfesa Umaru Pate a matsayin sabon Shugaban Jami’ar, bayan cikan wa’adin Shugaban Jami’ar na biyu, Farfesa Alhassan Gani na shekara biyar a kan kujerar.