Farfesa Soyinka ya caccaki Jonathan
Farfesa Wole Soyinka ya soki lamirin yadda Gwamnatin Shugaba Goodluck Jonathan ta daura yaki da Najeriya, inda ya caccake shi kan keta doka Soyinka, wanda ya gabatar da jawabi ga manema labarai a Legas, ya cacaccaki Sufeto Janar na ’Yan sanda, Suleiman Abba, wanda ya ce irin ‘abin kunya da yake tafkawa ya kai ga […]
Farfesa Wole Soyinka ya soki lamirin yadda Gwamnatin Shugaba Goodluck Jonathan ta daura yaki da Najeriya, inda ya caccake shi kan keta doka
Soyinka, wanda ya gabatar da jawabi ga manema labarai a Legas, ya cacaccaki Sufeto Janar na ’Yan sanda, Suleiman Abba, wanda ya ce irin ‘abin kunya da yake tafkawa ya kai ga bacin suna.’
A cewar Soyinka, Gwamnatin Shugaba Jonathan ta yi kaurin suna fiye da ta Buktanasar (Nebuchadnezzar) da aka ambace shi a Littafin Baibul, wato Sarkin da ya yi mulki a Daular Babilon a shekara 562 zuwa 605 kafin zuwan Yesu Almasihu, amma a karshe Ubangiji ya kaskantar da shi, ya wulakanta, saboda jiji da kansa da kama-karya. Soyinka ya soki Jonathan kan cewa shi ke da alhakin karya dokar da ’yan sanda suka tafka a rikicin da ya auku a Majalisar kasa.
“Babu abin da ya fi muni a shugabanci kamar kaskantar da tafarkin da ya kai shugaba ga gaci, tunda wannan shi ne abin da al’ummar kasa ke ta gani tsawon lokaci a sassa daban-daban, inda a baya-bayan nan aka kai wa ’yan majalisa hari, al’amarin da ya kasance babbar wauta da rashin hankali. Dangane da tabargazar kwanan nan, a iya cewa daya ce kawai daga cikin ayyukan keta doka, domin har yanzu Shugaba Goodluck Ebele Jonathan yana ci gaba da shammatar mu ta hanyoyi da dama da ba kowa ke iya hasashen aukuwarsu ba, a cewar Soyinka.
Yace, duk da cewa tsarin dimokuradiyya ne ya dora Jonathan bisa mulki, amma ayyukansa na nuni da cewa shi mai kama-karya ne. Ya buga misalai kan abubuwan da suka auku a kungiyar Gwamnanoni, inda ka raba kansu da Shugaban kasa ya rinjayar da gwamnoni 16 a kan 19.
Farfesa Soyinka ya kuma ragargaji Shugaban kasa kan yadda yah an gwamnonin ’yan jam’iyyar adawa shiga Jihar Ekiti don yakin neman zaben tsohon Gwamna Kayode Fayemi a watan Yunin da ya gabata, inda ya ce, wannan al’amarin kadai ya isa a ce Jonathan ya zama mai kama-karya, wanda ke sanya jami’an tsaro su keta haddin masu rike da mukaman hukuma.
Ya ce manufar nada Suleiman Abba a matsayin Sufeto Janar din ’yan sanda, ita ce cimma burin Shugaba Jonathan na son rai. Saboda haka ya ce, abin takaici ne Shugaba Jonathan ya umarci ‘yan sanda su hana ’yan majalisa shiga majalisar kasa, a ranar da ya kamata su zauna su tattauna kan yiwuwar kara wa’adin dokar ta-baci a yankin Arewa maso Gabas. Ya ce, Suleiman Abba, shi ma ya daura yaki a kan Najeriya, kamar yadda shugaban kasa ya yi, sannan ya yi raga-raga da tsarin dimokuradiyya a kasar nan.
“Abu na baya-bayan nan shi ne, ganin yadda wadanda ya kamata su bai wa doka kariya suka kaddamar da yaki da jama’a. Irin wadannan ma’aikatan gwamnati ya akamata a hukunta su, a gurfanar da su (a kotu), sannan a yi musu hukuncin da ya dace ga duk wanda ya ci amanar kasa. Abba bai bata lokaci ba wajen dabbancin amfani da karfin iko, amma ’yan Najeriya suna da zabi, kan ko su amince ko kuma su nuna turjiya. Kada dai mu saki layi, yanzu dai an gindaya mana iyaka. Don haka, dole ne mutane su yanke wa kansu hukuncin yarda ko kin amincewa,” inji Soyinka.
Soyinka ya ce:” Ta’asar da jami’in ’yan sanda ya tafka ta fi gaban abin kunya, har ta kai ga bacin suna An lalat aharkokin mulki, ta yadda duk wnai mai snaye da kayan sarki zai iya bugun kirji ya dakatar da zababben wakalin mutane.”
Wannan mashahurin masani da ya taba samun lambar yabo ta Nobel, ya yabi ’yan majalisar, wadanda suka yanke hukuncin tsallaka Katanga don su samu damar aiwatar da ayyukansu na tsara dokoki, inda ya yi nuni da cewa bai kamata a ce kafafen yada labarai sun soki lamirinsu.
“Haura shinge da Katanga don aiwatar da aikin da ya rataya a kansu, dole ne a kawar da maganars a irin wannan muhimmin lokaci na su. Dole ne a yaba musu, kada a aibata su. Idan za a alakanta wani da abin kunya, to Sufeto Janar na ’yan sanda, saboda bautar biyayyar da yake yi wa kullin makirci da keta doka wajen bin umarnin da babu su a cikin kundin tsarin mulki,” a cewarsa.
Sai dai a martanin Shugaban kasa Goodluck Jonathan, ta hannun Babban Jami’i na musamman da ke taimaka masa kan harkokin hulda da jama’a, Doyin Okupe, ya ce Soyinka “ya bar jaki ne yana bugun taiki,” tunda ya san wadanda ke karya doka, amma ya kyale su da gangan.
Okupe ya ce Soyinka ya kasa bayyana wa Gwamnan Jihar Ribas Rotimi Amaechi gaskiya, wanda ya siffanta a matsayin “Jigon kasa a wajen keta doka da kasada ko ganganci a harkokin mulki.”
A cewar mataimakin shugaban kasar, Gwmanatin Jonathan na alfahari da cewa, “ita ce mafi saukin kai, wadda ke bin doka da jere wa masu musguna mata.”