Farfesoshi uku ’yan kasar Amurka sun Musulunta a Yola

kungiyar Musulmi ta Jami’ar Amurka a Najeriya (American Unibersity Nigeria AUN) da ke Yola fadar Jihar Adamawa ta yi abin tarihi inda wasu farfesoshinta mutanen Amurka uku suka musulunta. Wadanda suka Musuluntar sun hada Dokta Lionel Rawlins wanda tsohon ma’aikaci ne a bangaren masu kula da sojojin ruwa na Amurka kuma shi ne shugaban sashin tsaro […]

Farfesoshi uku ’yan kasar Amurka sun Musulunta a Yola
Farfesoshi uku ’yan kasar Amurka sun Musulunta a Yola

kungiyar Musulmi ta Jami’ar Amurka a Najeriya (American Unibersity Nigeria AUN) da ke Yola fadar Jihar Adamawa ta yi abin tarihi inda wasu farfesoshinta mutanen Amurka uku suka musulunta.
 Wadanda suka Musuluntar sun hada Dokta Lionel Rawlins wanda tsohon ma’aikaci ne a bangaren masu kula da sojojin ruwa na Amurka kuma shi ne shugaban sashin tsaro na Jami’ar AUN a yanzu, sai Dokta Gabriel Fruster wanda Darakta ne a sashin buga takardu (dab’i) na Jami’ar AUN da kuma Dokta Tristan Porbis wanda babban malami ne a jami’ar.
A ranar Juma’ar da ta gabata ne Limamin Masallacin AUN, Ustaz Dauda Bello ya gabatar da su ga masallatan da suka halarci masallacin, inda ya bukaci ’yan uwa Musulmi su taimaka musu a duk lokacin da suka hadu da abin da ya shige masu duhu game da Musulunci.
 Ustaz Dauda Bello ya yi kira ga Musulmi su kula da addininsu tare da nuna kyawawan misalan addinin ta yadda wadansu za su yi kwadayinsa har su yi sha’awar shigowa Musulunci.
Farfesoshin uku dai sun ce sun yanke shawarar shiga Musulunci ne bayan sun yi bincike mai zurfi kan addinin Musulunci. Sun ce sun fahimci cewa Musulunci hanya ce mafi sauki a rayuwar kowane dan Adam.
Kakakin kungiyar Musulmin Jami’ar AUN, Malam Abdullahi Njidda Damare ya ce karbar Musuluncin farfesoshin uku ya kara wa addinin karfi da kuma karuwa a yawa.
Malamin ya yi kira ga Musulmi su natsu da kuma yin kyawawan ayyukan da za su kwadaitar da wadanda ba Musulmi ba su rika shiga addinin Musulunci.