Farfesun ganda

Assalamu alaikum uwargida tare da fatan alheri. A yau na kawo muku yadda ake hada farfesun ganda, walau gandar akuya ko ta shanu domin sanya kunnen maigida motsi a kodayaushe.  Ina fatan kuma ana gwada wadannan girke-girke da muke kawo muku domin neman kwarewa a harkar girki.Abubuwan da za a bukata• Ganda•Attarugu•Albasa•Tumatiri• Nutmeg•Tafarnuwa•Maggi• kori• Kayan […]

Farfesun ganda
Farfesun ganda

Assalamu alaikum uwargida tare da fatan alheri. A yau na kawo muku yadda ake hada farfesun ganda, walau gandar akuya ko ta shanu domin sanya kunnen maigida motsi a kodayaushe.  Ina fatan kuma ana gwada wadannan girke-girke da muke kawo muku domin neman kwarewa a harkar girki.
Abubuwan da za a bukata
• Ganda
•Attarugu
•Albasa
•Tumatiri
• Nutmeg
•Tafarnuwa
•Maggi
• kori
• Kayan kamshi
• Tukunyar dafa ganda (Pressure cooker)
Hadi
Bayan uwargida ta wanke ganda da ruwan kanwa domin cire karni, sai ta  zuba a tukunyar dafa ganda domin samun farfesu mai laushi . Sai ta yayyanka albasa da tumatiri. Ta jajjaga attarugu daidai misali da tafarnuwa. Sai ta daka garin nutmeg ta zuba da maggi da kori da thyme. Sannan sai ta zuba ruwa daidai misali ta rufe. Sai ta jira ya nuna na tsawon awa daya. Sannan ta sauke.
Ana son cin wannan girkin da safe ko da dare. Wannan irin girki, shi ne, wanda ya fi dacewa da masu son rage kiba. Domin ganda ba ta dauke da sinadarin dada kiba, illa a ci kawai don dadi. Tafarnuwar da aka sanya a cikin girkin na rage mura da kuma kare wadansu cututtuka kamar su mura da sanyi da sauransu. Ana son a rika girka irin wannan girki ga maijego, domin samun ruwan nono da karin koshin lafiya. Da fatan wannan girki zai sanya kunnen mai gida motsi. Ga dadi ga kuma arhar kayan girki. A sha lagwada lafiya.