Farfesun Kaza Mai bota
Kayan haxi . Kaza Bota . Kayan miya . Tafarnuwa . Citta xanya . Kayan qanshi . Sunadarin dandano Yadda ake haxawa: Da farko uwargida za ki sami kaza, amma tsoka, sai ki yanka qanana sannan ki wanke ki sa a tukunya ki zuba tafarnuwa da citta da sauran kayan qanshi da albasa. Sa’annan […]
Kayan haxi
. Kaza Bota
. Kayan miya
. Tafarnuwa
. Citta xanya
. Kayan qanshi
. Sunadarin dandano
Yadda ake haxawa:
Da farko uwargida za ki sami kaza, amma tsoka, sai ki yanka qanana sannan ki wanke ki sa a tukunya ki zuba tafarnuwa da citta da sauran kayan qanshi da albasa.
Sa’annan sai ki kuma zuba xan gishiri da sinadarin xanxano, sa’annan ki rufe ki bar shi ya dahu.
Sai ki sami wata tukunyar ki zuba yankakkun kayan miya a ciki sai ki rufe, idan ya dahu sai ki juye a cikin bilenda ki markaxa.
Sai ki sami tukunya ki zuba bota, idan ta narke sai ki xauko markaxaxxen kayan miyar, ki juye akai, sannan ki xauko kazar nan ki juye akai sai ki qara zuba sinadarin xanxano sai ki juya ki rufe tukunyar har ya haxu. Shi kenan farfesunki ya haxu.