Farin kuduri shi ke haifar da farar nasara

Assalamu alaikum, ya ku ma’abuta karanta wannan muhimmin fili na Sinadarin Rayuwa. Yau kuma za mu dauki sabon maudu’i kuma sabon salo, wai kaza ta ji shikar dare.A kan maudu’inmu na yau kuma, za mu duba yadda kyakkyawan kuduri ke taka rawa wajen cin nasarar dan Adam a rayuwarsa. Domin kuwa kamar yadda fitaccen marubucin […]

Farin kuduri shi ke haifar da farar nasara
Farin kuduri shi ke haifar da farar nasara

Assalamu alaikum, ya ku ma’abuta karanta wannan muhimmin fili na Sinadarin Rayuwa. Yau kuma za mu dauki sabon maudu’i kuma sabon salo, wai kaza ta ji shikar dare.
A kan maudu’inmu na yau kuma, za mu duba yadda kyakkyawan kuduri ke taka rawa wajen cin nasarar dan Adam a rayuwarsa. Domin kuwa kamar yadda fitaccen marubucin nan, Alhaji Bashir Tofa ya ce, ‘tunaninka kamanninka, makomarka tana hannunka.’ Haka rayuwa take, duk abin da mutum ya zaba ko yake son ya zama, zai iya zama, musamman ta hanyar sarrafa tunaninsa da kudurorinsa domin cin ma abin da yake son cin mawa a rayuwa.
Abin da ya kamata mu sake fahimta game da rayuwa shi ne, a duk lokacin da ka kudurta a ranka cewa kana son samun wani abu mai kyau, to kuwa mai kyan za ka samu, haka kuma idan ka kudurta cewa mummuna kake son samu, to, kuwa mummunan za ka samu; babu dadi kuma babu ragi.
Tun farko, idan mutum na so ya zama wani shugaba mai kima kuma wanda jama’a ke ba daraja da girma, shugaba mai adalci da gaskiya; mutum zai iya zama irinsa, musamman saboda a tarihin duniya, an sha samun irin wadannan shugabanni a baya, kuma a halin yanzu ma akwai irinsu a sako-sakon duniyarmu. Ke nan, tun da an taba samu, to kai ma za ka iya zama irinsu, musamman idan ka kudurta a ranka cewa, ‘ni kuwa ina son zama irin wannan shugaba.’ Da zarar ka saka wannan kuduri a ranka, to ka samu rabin nasarar burinka, saura rabin na nan wajen bin hanyoyin da suka dace domin idasa nufinka ko kudurinka.
Wani abu da kuma za ka yi shi ne, za ka jajirce wajen neman sanin matakai da hanyoyin da irin wadannan shugabanni da kake son zama irinsu suka bi har suka cin ma kasancewa shugabanni nakwarai. Idan ka gano irin wadannan matakai, sai ka bi su sau da kafa, da hakuri ba da garaje ba; da ikon Allah sai a wayi gari ka zama hamshakin shugaba mai gaskiya da adalci, shugaba abin kwatance, abin girmamawa ga jama’a.
Haka kuma, daga ranar da ka sanya kudurin son zama shugaba mai adalci, tun daga ranar za ka fara bin turbar shugabanci a cikin al’amuranka. Da farko, za ka fara ne da jan linzamin shugabancin zuciyarka, watau ka zama kai ke shugabanci da kanka. Ka koyi hana jikinka bin ummurnin karkatattun kudurorin da zuciyarka ta bijiro maka da su. Ka koyi amfani da kwakwalwarka wajen zabin abubuwan kirkin da za su kai ka ga cin ma burinka.
Idan ka samu nasarar jagorancin zuciyarka, za ka samu wata tarbiyya ta musamman, wacce za ta fitar da kai daban da sauran jama’a, kasancewar mafi yawan mabiya, ko in ce talakawan da ake mulka, ba su mallakar tunanin zukatansu da kwakwalwarsu tun da farko, shi ya sanya za su dogara da tunanin wani, wanda haka zai sanya su zama abin da ake kira bi-ta-zai-zai. Ke nan za su zama masu bin kudurori da ra’ayoyin wadanda suke bi, watau wanda ya zama shugaba a gare su. Idan shugaba gurbatacce ne, haka za su kasance su ma, watau gurbatattu. Idan an yi sa’a kuwa shugaban na kirki ne, sai su zama mabiya na kirki.
Kamar yadda ta kasance ka zama mai mulkin zuciyarka da kyakkyawan tunaninka, to sai kuma ka ci gaba da aiwatar da wannan kuduri naka a inda ka samu kanka. Idan magidanci ne kai, sai ka fara mulkin iyalanka cikin adalci da gaskiya. Wannan zai sanya ka samu matsayi na musamman a gidanka, za ka zama shugaba abin koyi, wanda ake ba daraja a gidanka. Idan kuma ka fito waje, cikin abokan aiki ko abokan sana’a, nan ma sai ka rika mu’amala cikin jagoranci na gaskiya da adalci. Ka yi watsi da duk wata halayya ko dabi’a da za ta jawo maka kaskanci a cikin abokan huldarka. Na sha maka alwashi, madamar ka dauki wannan turba, to tabbas ka kama hanyar zama irin wannan shugaba da ka kudurta wa zuciyarka.
Idan ka tuna da abin da na gaya maka a baya, ba lokaci daya ne za ka cin ma nasarar wannan kuduri naka ba, a’a, sai sannu a hankali, tare da aiwatar da halayen kwarai a al’amuranka na wannan lokaci ko matsayin da kake ciki. Haka abin zai ci gaba da gudana, daga wannan mataki na rayuwa zuwa wancan. Kafin ka kai ga tsufa, sai ka ga ka zama irin shugaban da kake bukata a zamaninka.
Ba ta fuskar shugabanci kadai za ka iya samun nasara ba, haka abin yake idan kana da kudurin zama wani gawurtaccen malami ko gawurtaccen likita ko bunkasasshen dan kasuwa. Idan ma kana son zama babban manoni ko dai wani hamshakin magabaci ta fuskar wani nau’in al’amurin rayuwa, duk dai matakan da za ka dauka ke nan, kamar yadda muka ba da misali a baya.
Darasinmu na yau shi ne, za ka iya samun nasarar rayuwa ta hanyar bin kuduri ko burin da ka sanya wa ranka. Ta hanyar bin kyakkyawan kuduri, za ka iya samun kyakkawan matsayi a rayuwa, kamar kuma yadda za ka iya zama gurbatacce, karkataccen gora marar amfani ga al’umma ta hanyar bin gurbatacce ko karkataccen kuduri. Allah Ya sanya mu sanya kudurorin kwarai a zukatanmu, kuma mu samu nasarar cin ma burace-buracenmu nakwarai a rayuwarmu, amin.

Dausayin kauna

kalubale, matsala ko cikas da muke fuskanta a harkar soyayya (3)

Tafiya sannu-sannu, ga shi har mun shiga mako na uku cikin maudu’inmu na jin kalubale, matsala ko cikas da muka ko muke kan fuskanta a harkar soyayya. A yau kuma za mu fara da sakon Basiru Suru Tudun Jukun Zariya (08176134706), wanda ke cewa: “FDk, ni ina cikin matsala; don na shafe shekara uku ina dakon soyayya amma mahaifinta ya ce ba zan aure ta ba, duk da ya san irin dawainiyar da na yi a tsawon zama na da ita. Gaskiya an yaudare ni, koda dai na san ba ta da laifi, don ta rike mini amana, ma haifinta ne ya takura ni kuma ban san abin da na yi ba. Ga shi yanzu bikin nata bai fi saura wata daya ba. Ma’abota soyayya, a taimake ni da mafita.”
Sai kuma sakon Ameenah (RUK) Kaduna (08030540531), tana cewa: “FDk, ni dai na sha wahala a soyayya, domin wanda muka kusan shekaru biyu muna soyayya, ko kadan babu alamar yaudara a tare da shi; sai lokacin da aka ce na fito da miji, sannan ne ya juya mini baya. Ku taya ni addu’a, Allah Ya ba ni masoyi na hakika, amin.”
Sai kuma Nasiru Muhammad Rjiyar Lemo Kano (08062674148), ya ce: “Babban kalubalen da na taba fuskanta dangane da harkar soyayya shi ne, a wani lokaci da ya wuce, na taba zuwa wajen wata yarinya da niyyar bayyana mata kaunata a gare ta amma sai ta dube ni ta ce wai za ta yi shawara. Babban abin da na kasa ganewa shi ne, surar jikina ce take da nakasu ko kuma ba ni da tsarin mijin da za ta aura ko kuma jan aji ne? To, in dai jan aji ne, to lallai ta sani cewa ni na ja makaranta.”
Shi kuwa Ishak Yunus K. (08130681142), a nasa sakon, cewa yake: “FDk, gaskiya ni masoyiyata gara ce, ga ta ’yar birni amma kana jin kalamanta za ka san bosoruwa ce. Tun daga yadda take washe baki in tana magana, za ka san kucaka ce. Amma fa ba don haka ba, in ka gan ta za ka yi zaton ’yar Indiya ce saboda kyau, fari, gashi da dadin murya. Don Allah FDk, ka isar wa ’yan uwa da ke Dausayin kauna su taya ni addu’ar Allah Ya gyara min ita.”
Ita kuwa Sadiyar Maisona (08036300751), korafi ta yi cewa: “A gaskiya wasu maza sun iya cin amana, sannan su yi fuska! Maza abin tsoro ne. Ku daina cin amana. Na gani a kaina, ni ma an yi min; ban ji dadi ba.”
Abdullahi Sa’id danhausa Kano (07035011450): FDk, fatan alheri ga masoyan gaskiya. A rayuwata Naseeba Auwal Boss ita ce mace kwallin kwal da zuciyata ta makance a kan son ta da kaunar ta maras adadi kuma ita ma ta so ni matsanancin so na gaskiya. Ba a banza na samu soyayyar ta ba, sai da na shekara biyu ina naci sannan ta amince da ni, sai da muka zama daya ni da ita; jinin jikinmu ya gauraya ya zama iri daya. Mun wuce hanta da jini wajen shakuwa, ta yarda da ni, kamar yadda kowane mai rai ya yarda da cewa zai mutu. Ta so ni irin zazzafan so, irin son da uwa take wa ’yarta kwaya daya tilo. Tana son farin cikina koda ran kowa zai baci. Tana cewa da ni ‘Yayana, ina son ka, in sha Allahu kai ne mijina, uban ’ya’yana!’ Na sakankance cewa na samu masoyiya ta har abada kuma mata a gare ni, kwatsam bayan shekara hudu da fara soyayyarmu ta yi min shigo-shigo ba zurfi. Ta daina yi min murmushi sai harara da kyara! Ta tsane ni, ta manta da ni, ta kore ni, ta ha’ince ni. Idan na ce mata ‘Gimbiya’ sai ta ce mini ‘Mujiya.’ Ta taba cewa da ni ni ne masoyinta na farko kuma na karshe. Ta taba zubar da hawaye a kaina. Ta taba yin kyautar ban mamaki sabo da an birge ni! Amma yanzu ta yi shagulatun bangaro da ni. Ruwa ya doki babban zakara, na yi, na yi ta fada min matsayina amma ta ki. Miskila ce!”
Haba Abdullahi, soyayyar shekara hudu? Wace irin soyayya ce wannan? Don Allah masoyan dandalin nan, ku gane mani hanya! – FDk.
Daga Hauwa’u Toro (08180812545), sakonta na cewa: “FDK, ina fatan kana lafiya. Maza mayaudara ne, macuta, marasa amana. Namiji ya yaudare ni, yaudarar da ban taba zaton zai min ba. Ni da soyayya yanzu sai dai in ga ana yi amma na yi ritaya!”
Wayyo! To Malama Hauwa’u, idan kin yi ritaya daga soyayya, sai kuma me, kiyayya? – FDk.
Sai kuma Bashir Muhammad Yahuza Gama: “Na kasance cikin yunwar son wata ’yar uwata, to amma daga ranar da na fada mata manufata sai ta daina kula ni kuma in na yi kiran layinta sai ta ki dauka kuma takan yi mani tes wai in tura mata da katin waya. Shin ta yaya zan bullo wa wannan al’amari, me take nufi ke nan?”
A gani na, yarinyar nan karama ce kuma tana da kunya. Tun da har za ta nemi abin hannunka, to ina zaton ta amince da bukatarka, sai dai kuma rashin wayau da ke tattare da ita ne ke damun ta. Allahu a’alamu, ko me kuka gani, jama’a? – FDk.
Daga Nasiru Albanin Bauchi (08167155483), yana cewa: “Masoya, ina muku fatan alheri! Hakika soyayya idan ta yi dadi, ta fi komai dadi, haka kuma idan ta yi daci, ta fi komai daci! A rayuwa, zo mu zauna ne, zo mu saba. Saboda haka ina jan hankalin ’yan uwana masoya da cewa mu zamanto masu hakuri, musamman ma yayin da aka samu sabani.”