Farin Magi Mara Alama Na Barazana Ga Lafiyar Al’umma —Masana
Masana kiwon lafiya sun nuna damuwa kan rashin ayyana sunan kamfani a wasu farin magi da kayayyakin abinci da dauke da shi da suke yawo a kasuwannin Arewacin kasar nan.
Masana kiwon lafiya sun nuna damuwa kan rashin ayyana sunan kamfani a wasu farin magi da kayayyakin abinci da dauke da shi da suke yawo a kasuwannin Arewacin kasar nan.
Sun kuma bayyana yawaitar wasu nau’ikan farin magi marasa dauke da suna a jikin mazubi da buhunasu a matsayin abin damuwa saboda illar da ke tattare da hakan.
Farin Magi, wato Monosodium Glutamate (MSG) ko sodium glutamate, abin sanya dandanon girki ne na glutamic acid, wanda ake samu a wasu nau’kan abinci ciki har da tumatir da cukwi.
Malam Salihu Muhsin, kwararre ne a fannin lafiya a Jihar Kaduna, ya shaida wa Aminiya cewa sinadarin farin magi marasa suna a jikin mazubinsu sun karade kasuwannin Arewacin Najeriya.
- Jerin hatsarin jiragen sojin Najeriya a 2023
- Khadijah Mai Numfashi ta tuba bayan dakatar da ita daga Kannywood
Ya ce “A Kaduna da wasu sassan Arewacin kasar nan ana fama da yawan ta’ammali da miyagun sinadarai da kayan abinci marasa inganci da suka hada da MSG, wanda kwararru a fannin kiwon lafiya suka fara nuna fargaba kan illolin da ke tattare da hakan.”
Ya ce yayin da Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC) da hukumar ingancin kayayyaki (SON), ke kan gaba wajen dakile illolin rashin ingancin kayayyaki, sun kuma mayar da hankali kan rarrabawa, tallace-tallace da amfani da samfurorin kayayyakin da suka dace.
“Har ila yau, sun shiga yaki da kaya marasa inganci a kasuwanni inda suka sha kama masu kera jabun kayayyaki ko marasa inganci.
“Wani abin bakin ciki ya faru a Kano inda mutane uku suka mutu bayan sun sha wani gurbataccen abin sha wanda gwajin NAFDAC ya nuna an samu karin sinadarai masu hadari a wajen hadawa, sannan biyu ne kawai daga cikin kamfanoni biyar da ke da hannu a badakalar ke da rajistar NAFDAC.
“’Yan Najeriya na bukatar su dora daga inda NAFDAC ta tsaya ta hanyar tabbatar da cewa kayayyakin da suke saya sun samu amincewar NAFDAC, ba bin arha ba.
“Kuma yana da mahimmanci a tabbatar da mahimman bayanai kamar ranar samarwa, ranar karewa ko lalacewar abu, sunan kamfani, amincewar NAFDAC, da sauran mahimman bayanai,” in ji shi.
Masanin ya sake nanata cewa akwai hadarin nau’in farin magi da ya ce ’yan kasuwa ke yi tare da tilasta wa mutane cin abinci mai dauke da shi.
“Wadannan monosodium glutamates da ba a rubuta suna a buhunansu ba, ba kamar manyan kamfanoni irin su Ajinomoto, Vedan da sauransu ba ne, waɗanda NAFDAC ta amince da su.
“Su ba za a iya gano masana’antunsu don bincika sahihancinsu ba kuma ana sayar da su ne da arba, wanda zai iya zama alamar rashin ingancinsu da dacewarsu da lafiyar ɗan adam.
“Dole ne kowane dan Najeriya ya sa ido kan kansa da sauran ’yan kasarsa domin dakile wannan ta’asa.
“Masu sayar da abinci ya kamata su kula da lafiyar kwastomominsu ta hanyar yin amfani da samfurori masu kyau wurin dafa abinci, haka ma matan gida da masu aikin gida.”