Farmakin da ’yan sandan kamaru suka kawo Najeriya

Farmakin da aka kai wa al’ummar Damare da ke karamar Hukumar Boki a Jihar Kuros Ribas, inda ’yan sandna Kamaru suka kawo mamaya a makon da ya wuce suna neman shugabannin yankin Ambzonia da ke fafutikar a ware ya keta haddin fadin dunkulalliyar Najeriya. Jami’an tsaron, wadanda yawnasu ya kai 80 an ruwaito cewa sun […]

Farmakin da ’yan sandan kamaru suka kawo Najeriya

Farmakin da aka kai wa al’ummar Damare da ke karamar Hukumar Boki a Jihar Kuros Ribas, inda ’yan sandna Kamaru suka kawo mamaya a makon da ya wuce suna neman shugabannin yankin Ambzonia da ke fafutikar a ware ya keta haddin fadin dunkulalliyar Najeriya. Jami’an tsaron, wadanda yawnasu ya kai 80 an ruwaito cewa sun kai mamaya a cikin al’ummar ake zaton ’yan Kamaru da ke yankin da ake amfani da Ingilishi mutum fiye da 5,000 sun samu mafaka cikin dare, ind asuka ci zarafi da kama dimbin ’yan gudun hijira.

3annan bas hi ne karo na farko ba da jami’an tsaron Kamaru suyka keta doka wajen kutsowa cikin Najeriya don kama wadanda ake zargi da fafutikar a ware. A Disambar 2017, an ruwaito yadda suka kwata irin wannan ta’ada, ta hanyar kutsawa ta kafar budaddun kan iyakokin da ke tsakanin Kamaru da Kuros Riba don kai farmaki a sansanin ’yan gudun hijira, inda suke neman ’yan yankin Ambazonia. Tsahintashinar da ke tsakanin ’yan Kamaru da Ambazonia wutar rikicin ta kara ruruwa ne a ranar 1 ga Oktobar 2017, yayin da wannan yanki da ke magana da harshen Ingilishi a Kudancin Kamaru ya tabbatar da ’yancin cin gashin kansa daga gwamnatin kasarsu da ke yankin Afirka ta tsakiya., inda aka yi nuni kan yadda gwmanati ke  nuna wariya da nbautar da al’umma.

A daidai lokacin da rikicin ke ruruwa fiye da mutum dubu 40 daga Kudnacin Kamaru suka tslalaka iyakar kasarsu zuwa Najeriya, musamman cikin al’ummomin da suke mu’amala da harshe guda da al’adu. A kullum tun da aka fara rikicin wadannnan ’yan gudun hijira na ta kwarara ba kawai a Jihar Kuros Riba ba, har ma da Jihohin Taraba da Binuwai da Akwa Ibom. Hukumomikn bayar da gajin gaugawa  a wadannan jihohin Najeriya suna daukar dawainiya samar da wuraren kwana da abinci ga dubban ’yan Kamaru da rikicin ya tarwatsa su. Abin a yi tur ne, ganin yadda jami’an tsaron Najeriya ke kyale ’yan sandan Kamaru ke keta doka su tsallaka iyakokinmu, su kama ’yan gudun hijirar da suka samu mafaka a fadin kasar nan.

Sashe na 2 91) na kundoin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999 9wanda aka yi wa gyara) ya tabbatar da kariyar fadin kasar nan, inda ya ce, “Najeriya dunkulalliya ce, wadda ba a wargaza karfin ikon kasarta daak sani sunan Tarayyar Jamhuriyyar Najeriya.” Rundunar Sojan Najeriya an ba su karfin ikon kare fadin kasar nan. Dokar Majalisar dinkin Duniya mai lamba 2625, wadda daukacin ’ya’yanta suka rattaba wa hannu a Oktobar 1970, ta ce, “fadin kasa ba zai kasance karkashin mamayar soja ta hanyar tursasa wa da karfi, wajen keta wannan doka. Fadin kasar ba zai kasance karkashin wata kasa ba, ta hanyar barazana ko nuna karfin soja. Ba za a mamayi fadin kasar ba sanadiyyar barazana ko amfani da karfi al’marin da doka ba za ta amince da shi ba..”

Daga wannan tanadi, babu wata kafa da ta bai wa jami’an tsaron Kamaru damar kutsowa cikin Najeriya su kama ’yan kasarta, wadanda aka dauka ’yan tayar da kayar baya. Abin da ya kamata a lura cewa Hukumomin tsaron Najeriya sun tabbatar da cewa kasar nan ba za ta tallafa ko amincewa da abin da ’yan Ambazonia na Kamaru ke aikatawa. Sai dai, wannan karamci bai kamata a dauka ya byar da damar yin kutse abin tuhuma da rundunar tsaronsu ta yi a Najeriya don kama masu laifi. Aiki ne da ya rtaya ’yan sandan duniya da ke bin kadin miyagun laifuka da aka aikta su shiga tsakani a kowace kasa da ake bukatar kama masu laifin da suka samu mafaka a sauran kasashen.

Hurumin Majalisar dinkin Duniya ne ta umarci ‘’yansandan duniya cewa, “karfin iko da aikin da ya rataya kan ‘’yan sandan duniya na “INTERPOL” shi ne su tallafa wa ’yan sanda da hukumnomin tabbatar da doka a duakacin kasashe 186 da ke cikinta a kokarinsu na shawo kan miyagun laifuka dabinciken miyagun ayyuka da kyau yadda zai yi tasiri. Kamata ya yi a samu hadin gwiwar tsaro musaman ta hanyar amfnai da ’yan sandan dunoiya na ‘INTERPOL’ a tsakanin ’yan sandan kan iyaka, tare da bayar da tallafin gwmanati  da kungiyoyin gwamnatatoci da kungiyoyi da hukumomi wajen aiwatar da ayyukan da ke manufar shawo kan miyagun laifuka.”

Muna kira da kakkausar murya ga Gwmanatin Tarayyi da ta nuna rashin yardarta ga Gwmanatin Kamaru, ta soki lamirin keta haddin fadin kasar mu. Da jami’an tsaronta suka yi. Muna kira ga ’yan Ambazonia da Gwmanatin Kamatu da su yi tattaunawar sasanci, inda za su samar da matsayar sasanta rikicin siyasa da ya dabaibaye lamarin da ya haifar da wannan rikici. Duk da cewa nba ma goyon bayan tayar da kayar bayana aware a ’yar uwar kasarmu ta Afirka, ba za mu yadda da keta haddin dunkulalliyar kasarmu ba.