Farouk Lawan ya kwana a Gidan Yarin Kuje

Ya fara zaman wakafi bayan shekara tara da karbar rashawar $500,000.

Farouk Lawan ya kwana a Gidan Yarin Kuje

Tsohon Shugaban Kwamitin Majalisar Wakilai kan binciken badakalar tallafin man fetur, Hon. Farouk Lawan ya kwana a Gidan Yarin Kuje, bayan kotu ta yanke masa hukuncin daurin shekara bakwai.

Babbar Kotun Abuja ta samu Farouk Lawan da laifin karbar rashawar Dala dubu dari biyar a lokacin da yake jagorantar kwamitin, daga hannun Femi Otedola, babban dan kasuwar man fetur, wanda kwamitin ke binciken kamfaninsa na Zenon Oil a lokacin.

Majiyarmu a Gidan Yarin Kuje ta ce, “Tabbas kai tsaye aka kawo shi (Farouk Lawan) nan daga kotu. Daga yau (Talata), ya fara zaman wakafi har ya kammala, sai dai idan ya daukaka kara ya kuma samu nasara a karar da ya daukaka.”

Farouk Lawan ya shiga sahun manyan shugabannin siyasar Najeriya da  ke zaman wakafi a Gidan Yarin Kuje, ne bayan shekara tara da fara shari’ar zargin nasa.

Babbar Kotun da ke zamanta a Apo, karkashin jagorancin Mai Shari’a Angela Otaluka ta samu tsohon dan majalisar da laifuka uku da ake tuhumar sa, na karbar rashawar ta $500,000 a shekarar 2012.

Tun daga lokacin aka yi ta kwan-gaba-kwan-baya a kotuna har, da Kotun Koli.

Babu tuhuma a kan Otedola

A yayin da aka yanke masa hukuncin da ya kai shi ga zaman kaso ga Gidan Yarin na Kuje da ke wajen garin Abuja, babu wata tuhuma da aka shigar a kan Otedola, wanda ya ba da nagoron.

Lauyoyi sun ce rashin tuhumar Otedola ya yi daidai, saboda jami’an tsaro sun yi yi amfani da dan kasuwar ne domin dana wa tsohon dan majalsiar tarko.

A lokacin zaman kotu, Otedola ya shaida mata cea hukumar tsaro ta DSS ce ta ba shi kudaden domin yi wa Lawan gadar zare.

An yake wa Lawan hukuncin ne kan karbar Dala 500,000 a matsayin wani kaso daga cikin Dala miliyan uku da ya bukaci Otedola ya bayar domin a cire sunan kamfanoninsa daga wadanda ake bincike kan badakalar tallafin man fetur.

Mai Shari’a Otaluka ta ce hujjojin da lauya mai shigar da kara, Adegboyega Awomolo (SAN), ya gabatar sun tabbatar da almundahanar da laifin wanda ake zargin da neman karbar cin hancin Dala miliyan uku.

“Yanzu aiki ya rage ga wanda ake zargin ya kore hujjojin da aka gabatar a kansa,” inji ta.

Kasa wanke kai

Ta kara da cewa wanda ake zargin ya gaza gabatar da wani mai suna Honourable Ribadu ko wani daga cikin mambobin kwamitin domin tabbatar da ikirarain da ya yi cewa ya karbi kudaden ne da nufin fallasa Otedola.

Ta ce wadannan mutane na da muhimmance a gare shi domin tabbatar da ikirarin da ya yi.

“Hujjoji sun tabbata cewa wanda ake zargin ya nemi cin hancin Dala miliyan uku, kuma ya karbi Dala 500,000 a lokuta biyu daban-daban daga hannun Femi Otedola,” inji Mai Shari’a Otaluka.

Don haka ta yi watsi da ikirarin Lawan cewa ya karbi $500,000 din ne domin kafa shaida cewa Otedola na so ya saye shi da ’yan kwamitin da ke binciken.

Daga nan ta yanke masa hukuncin daurin shekara bakwai a gidan yari, tare da umartar sa da ya mayar wa Gwamnatain Tarayya $500,000 da ya karba a hannun Otedola.

Mai Shari’a Otaluka ita ce alkali ta uku da ta saurari shari’ar tun daga lokacin da aka faro ta.

Alkalin da ya fara sauraron karar ya samu daukaka zuwa Kotun Daukaka Kara, na biyun kuma ta janye daga sauraron shari’ar bayan Lawan ya zarge ta da nuna son rai.

Zai iya daukaka kara

A yayin da aka tafi da shi zuwa gidan yari, lauyoyi sun ce har yanzu yana da damar daukaka kara, har zuwa Kotun Koli, zai kuma iya neman beli.

Kawo yanzu dai ba a ji daga bakin lauyansa, Mike Ozekhome (SAN), game da mataki na gaba da zai dauka ba.

Mutane na bayyana mabambantan ra’ayoyi game da lamarin, wasu ke cewa an yi adalci, wasu kuma ke ganin hau ce ta hau shi, saboda rikicin shugabanci a lokacin da yake Majalisar.

Wani tsohon jami’in DSS ya ce abin da hukumar ta yi ba sabo ba ne a tsarin aikin.

Daga Clement A. Oloyede (Kano) da Sagir Kano Saleh da Ismail Mudashir, Abbas Jimoh da  Hamisu Kabir Matazu da Idowu Isamotu.