Fasa aikin Hajji: Za a fara mayar wa maniyyata kudadensu

Hukumar Alhazai ta Abuja ta ce ta shirya mayar wa maniyyata kudadensu.

Fasa aikin Hajji: Za a fara mayar wa maniyyata kudadensu

Maniyatta aikin hajji

Hukumar Kula Jin Dadin Alhazai ta Birnin Tarayya, ta ce za ta fara mayar da kudaden maniyyatan shekarar 2021 da ke son karbar kudaden nasu.

Mai magana da yawun hukumar, Muhammad Aliyu ya sanar a ranar Alhamis cewa za a mayar da kudaden ga masu bukatarsu ne sakamakon soke aikin Hajjin 2021 da gwamnatin kasar Saudiyya ta yi a makon jiya.

  1. Mahara sun kashe dan sanda sun sace dan China
  2. ’Yan bindiga sun kashe mutum 26 a kauyen Zamfara

Aliyu ya ce maniyyata 1,964 da suka biya kudaden kujera don yin aikin Hajji na da ’yancin karbar kudadensu, idan suna bukata, kamar yadda Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON) ta umarta.

Ya kara da cewa wadanda suke son barin kudadensu zuwa Hajjin 2022 za su iya adana kudaden nasu a hannun Hukumar kuma su samu fifiko a wurin yin rajista.

Ya shawarci masu son karbar kudadensu da su tura takardun neman kudaden, tare da bayanan asusun bankinsu ga Daraktan Hukumar, su kuma karbi shaida don a sanya musu kudadensu a banki, saboda babu wasu kudi da za a biya a hannu.

Aliyu ya ce za kuma a iya gabatar da takardun neman kudaden ga jami’an yanki da ke Kananan Hukumomi inda aka fara biyan kudaden.

Wadanda ba su da asusun ajiyar banki kuma za su iya ba da bayanan asusun bankin wani nasu da za a saka musu kudadensu.