Fasahar intanet ta cika shekaru 25 (2)

Hypertedt Transfer Protocol (HTTP):  Wannan kuma wata ka’idar sadarwa ce  (Communication Protocol) da ke bai wa mutum damar isa ga nau’ukan bayanai da ke wata kwamfutar da ke wata uwa duniya daban, ta hanyar amfani da manhajar lilo, wato: “Browser” ke nan.  Wannan na yiwuwa ne ta dayan hanyoyi biyu; ko ta hanyar shigar da […]

Fasahar intanet ta cika shekaru 25 (2)
Fasahar intanet ta cika shekaru 25 (2)

Hypertedt Transfer Protocol (HTTP):  Wannan kuma wata ka’idar sadarwa ce  (Communication Protocol) da ke bai wa mutum damar isa ga nau’ukan bayanai da ke wata kwamfutar da ke wata uwa duniya daban, ta hanyar amfani da manhajar lilo, wato: “Browser” ke nan.  Wannan na yiwuwa ne ta dayan hanyoyi biyu; ko ta hanyar shigar da adireshin gidan yanar sadarwa (website) kai tsaye a jikin manhajar lilo – misali, ka shigar da adireshin Google: www.google.com – ko kuma ta hanyar latsa wani bayani mai dauke da adireshi a shafin sadarwa da ka ci karo da shi.  Duk wani bayani da ka dora beran kwamfutarka (Mouse) a kai ka ga ya canza launi ko an masa layi a kasansa, ko kuma dan manunin beran kwamfutar (mouse pointer) ya koma dan karamin hannu, to, kana matsa wannan bayani ko kalma za a zarce da kai wani shafin yanar sadarwa ne kai tsaye.  Wannan ka’ida tana gine ne a jikin kowace manhajar lilo.  Shi yasa, kana shigar da adireshin nan take za a zarce da kai, muddin akwai tsarin sadarwar Intanet a kan waya ko kwamfuta ko na’urar da kake kai.  Asalin adireshin kowane gidan yanar sadarwa shi ne: http://www.gidanyanarsadarwa.com.  bangaren farko shi ne: http://.  bangare na biyu shi ne: www.  bangare na uku shi ne: gidan yanar sadarwa.com.  Idan ka hade su duka, za a zarce da kai.  Idan ka cire bangaren farko, za a zarce da kai.  Haka ma idan ka cire bangaren farko da na biyu, ka shigar da bangare na uku kadai, duk za a zarce da kai.
Bayan samar da wadannan manhajoji da ka’idojin sadarwa, daga baya Farfesa Tim ya kara gina wasu manhajoji guda biyu da suka yi tasiri matuka.  Manhajar farko ita ce: WorldWideWeb.app, wanda manhaja ce ta lilo, wato: “Browser.”  Sai manhaja ta biyu mai suna: httpd, ita kuma manhajar uwar garke ce, wato: “Web Serber Application.”  Zuwa karshen shekarar 1990 aka kaddamar da ayyukan Farfesa Tim a cibiyar CERN, inda aka fara amfani da wadannan ka’idoji da manhajojin sadarwa wajen aikawa da karbar bayanai cikin sauki.  Shekara daya bayan haka kuma aka kaddamar da tsarin gaba daya ga duniya, inda aka gayyaci masana kimiyya wajen gwaji da kuma mu’amala da su.  Wannan ya faru ne daga ranar 23 ga watan Agusta, 1991; hakan ya kawo mu shekaru 25 ke nan daga wancan lokaci.
Da ya ga wannan fasaha ta Intanet ta ci gaba da habaka kamar wutar daji, sai ya yi tunanin cewa, tunda asalin fasahar na hannun cibiyarsu ne, kuma hakki ne na mallaka, za a iya samun matsala nan gaba.  Domin duk wanda ke bukatar fasahar dole ne ya nemi izni.  Hakan kuwa, a tunanin Farfesa Tim, zai iya kawo tsaiko wajen cimma burinsa na inganta hanyoyi da tsarin samuwar ilimi da bayanai cikin sauki a duniya.  Ga abin da ya ce dangane da haka:
“Da a ce wannan fasaha (Intanet) ta kudi ce, (wacce aka gina don kasuwanci) wadda ni kadai na mallaka kuma nake iya bayarwa, da har yanzu ba a kai ko’ina wajen habbaka ta ba.  Babu yadda za a yi ka ce wata haja ta kowace, amma ka ajiye ta wurinka kai kadai.”
Wannan mahanga ta Farfesa Tim ba ta takaitu ga fadin baki kadai ba, domin a shekarar 1993, cikin watan Afrilu in ban mance ba, ya bukaci hukumar cibiyar CERN da ta mika hakkin mallakar wannan fasaha da ya kirkira ta zama kyauta ga duk mai bukata a duniya, a ko’ina yake.  Hakan ya kara haifar da ci gaba sanadiyyar gamayyar masana da kirkire-kirkire da suka biyo baya babu kakkautawa.  Domin duk wanda Allah ya hore masa sani a wannan fanni, zai iya daukar wannan fasaha, ya kayatar da ita, ya kuma mallake ta kyauta; idan ma sayarwa yake son yi, duk zai iya.  An mallaka masa.
A shekarar 1994 sai Farfesa Tim ya yi hijira daga cibiyar CERN zuwa babbar cibiyar binciken kimiyya da ke kasar Amurka mai suna: “Massachusetts Institute of Technology,” ko “MIT” a gajarce.   Zuwansa wannan cibiya ke da wuya ya ci gaba da ayyuka masu kayatarwa.  A wannan cibiya ne ya samar da kungiyar masana masu tsarawa da inganta fasahar shafukan Intanet a duniya, mai suna: “World Wide Web Consortium,” ko “W3C” a gajarce.   Aikin wannan kungiya ta gamayyar masana, wanda shi yake shugabanta, shi ne samar da ka’idojin gina shafukan Intanet.  Wannan kungiya ya haifar da ci gaba matuka a fannin inganta shafukan Intanet a kwamfuta, sannan ya samar da sabon tsari mai kayatarwa da ya kunshi gina shafukan Intanet a wayar salula.  Duk kyale-kyalen da mai karatu ke cin karo da su a shafukan Intanet, a ko ina ne, wannan kungiya ce ta samar da ka’idojin da suka taimaka wajen samuwarsa cikin sauki.
Kafa kungiyar W3C ya taimaka wajen inganta tsarin samar da bayanai a duniya ta hanyar amfani da hanyoyi da na’urorin sadarwar zamani.  Ba wannan fanni kadai ba, hatta fannonin rayuwa wannan tsari ya shafe su, ya kuma yi tasiri a kansu, sosai.  Wannan ya bai wa fannin sadarwa yaduwa da gamewa; inda kowa ke iya mu’amala da fasahar Intanet a duk inda yake, ba ka bukatar neman izinin wata kasa a duniya.  Kamar yadda kuma babu wata kasar da ta mallaki makulli ko mabudin wannan fasaha, balle ta ce tana iya hanawa.  Tsarin ya haifar da rashin wariyar launin fata wajen yada bayanai.  Duk kasa ko al’ummar da ta mallaki fasaha da kwarewar da ake bukata wajen mu’amala da wannan tsari tana iya amfani da shi, babu tsangwama.  Sannan ya samar da hadakar masana, wadanda ke tattaunawa da juna daga ko’ina suke; kowa na iya tofa albarkacin bakinsa kan tsarin da ake son kaddamarwa, kafin a tabbatar  ko zartar da shi.  Wannan ya haifar da wani tsari gamamme, wanda kowa ya amince da shi.  A bangaren kere-kere kuma, an samar da na’urorin sadarwa daga bangarorin duniya daban-daban, amma masu fahimtar harshe da lugga iri daya, duk bambance-bambancensu.  Misali, da kwamfutar da aka kera a kasar Amurka, da wacce aka kera a kasar Indiya, da wacce aka kera a kasar Sin, da wacce aka kera a kasar Finland, duk suna iya fahimtar juna wajen aikawa da karbar bayanai.  Kowacce ana iya amfani da ita wajen hawa Intanet, da karbar sakon Imel, da kowane irin harshe ne kuwa.
A karshe, tallafin da Farfesa Tim Bernes-Lee ya bayar a fannin inganta fasahar Intanet a duniya ba karama bace.  Domin kokarinsa bai tsaya kan fannin sadarwa kadai ba, ya tallaka har zuwa fannin siyasa, da shugabanci, da ilimi da kuma al’adu.  Wannan ke nuna mana cewa lallai Farfesa Tim Bernes-Lee, wanda har yanzu yana nan da ransa, ya cancanci lakabin da aka ba shi mai take: “Baban Intanet.”
Ba mu gushe ba muna fa’idantuwa da wannan fasaha mai matukar tasiri. Fata dai Allah Ya sa mu mallaki hankulanmu, mu bude idanunmu, mu wasa kwakwalenmu, wajen gani da nazari kan abin da zai amfanemu, duniya da lahira, amin.
Jama’a, (HAPPY INTERNAUT DAY)!