Fasakwauri: Kwastam sun ce babu wajen buya ga masu laifi

Shugaban Kwastom na Jahar Adamawa da Taraba, Francis Adetoye ya jinjina wa Shugaban Kwaston na kasa, Kanar Hameed Ali saboda daukar tsauraran mataki a kan masu gudanar da saye da sayarwa ba a bisa tsarin dokar kasa ba, wadda a cewarsa hakan na haddasa ci baya ga kasa kuma za su yi koyi da daukar […]

Fasakwauri: Kwastam sun ce babu wajen buya ga masu laifi

Shugaban Kwastom na Jahar Adamawa da Taraba, Francis Adetoye ya jinjina wa Shugaban Kwaston na kasa, Kanar Hameed Ali saboda daukar tsauraran mataki a kan masu gudanar da saye da sayarwa ba a bisa tsarin dokar kasa ba, wadda a cewarsa hakan na haddasa ci baya ga kasa kuma za su yi koyi da daukar wannan matakin wajen damke dukkan masu laifi, domin a cewarsa “babu wajen buya ga masu laifuka.”

Francis ya ce shigo da kaya ba a kan tsarin doka ba, na janyo ci baya ga kasar nan da kuma hana kasar samun ci gaban da ya kamata. Ya bayyana hakan ne ga manema labarai a lokacin da ya gayyace su domin tattaunawa a kan harkokin shigo da kaya zuwa Najeriya ba ta hanyar da doka ta tsara ba.

Sannan sai ya gargadi masu aikata wannan aikin da su nisanci yinsa, domin wannan ba sana’a ba ce illa aikata laifi wadda idan an kama mutum zai fuskanci fushin hukuma. Ya kara da cewa burin Shugaba Muhammadu Buhari shi ne ganin cewa an sami cigaba akan tattalin arzikin kasar, wadda har za a iya gasar wannan tattalin arzikin da wadansu kasashe a duniya.

Adetoye ya ce ya kamata a tallafa wa manoma wadanda suke da kananan karfi, domin ba su damar shuka da girbi da kuma sayar da hatsinsu, yin hakan zai rage matsalolin shigar da kaya ba bisa ka’ida ko ya saba wa doka ba.

Haka kuma ya nuna godiyarsa ga Gwamnan Jahar Adamawa, Muhammadu Jibrilla Bindow da gwamnan Jahar Taraba, Darius Ishaku game da goyon bayan da suke bai wa jami’an nasa wajen cimma burinsu na kame masu laifi.

Ya kara da cewa ofishinsu na Jahar Adamawa da Taraba sun samar da kudaden shiga kimanin miliyan 48 daga Watan Janairu duwa Maris na wannan shekara ta 2018 wadda suka samo daga hatsi, sannan sun kame hauran giwaye 55 wadda a kalla za ta kai naira miliyan hamsin.

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya